Barka Da Zuwa Shafin Imam al-Asr (ATFS)

"Muhammad Awwal Bauchi Na Muku Barka Da Zuwa, A Sha Karatu Lafiya, Ina Sauraron Karin Bayani Da Shawarwarinku

Kashin Farko

Zababbun Sahaba

Abin Koyin Mata
Muhimman Ranakun Musulunci
 


Al'amurran Yau Da Kullum

Ana Iya Ganin Karin Bayani Kan : Azumi da Abin Da Watan Ya Kumsa

 

Karya Tsagwaronta:
(Uba Ahmad Ibrahim Jos)

Tun kusan watanni biyu da suka wuce wani shafi a yanar gizo ya buga Wani labari dauke da hoto da ke cewa wata yarinya 'yar kasar Sultanatu Amman ta wulakanta Al-kur'ani mai girma Allah Ta'ala kuma ya nuna mata iyakarta ya mayar da ita dabba,wannan labari ba karamin yaduwa ya yi a kasashen larabawan da ma kuma sauran kasashen duniya masu yawa ba. wasu sun dauki labarin a zaman wata babbar mu'jiza ce daga Allah Ta'ala domin ya nunawa masu wasa da addini iyakarsu....... Karin Bayani


 

Zaben Iran: Sakon Iraniyawa Ga Bush:
(Muhammad Awwal Bauchi)

Masu iya magana sukan ce wai rana ba ta karya sai dai uwar 'ya ta ji kunya, ko ba a fadi ba fitowar da al'ummar Iran, kwansu da kwarkwatarsu, suka yi a ranar Juma'ar da ta wuce (17 Yuni 2005) don kada kuri'arsu a zaben shugaban kasa karo na tara ya kasance babban bugu ga makiya Juyin Juya Halin Musulunci na kasar da kuma gwamnatin Musuluncin da ke mulki a kasar. A wannan karon ma karfin al'umma ya sake nuna kansa a fili duk kuwa da kiraye-kirayen da masu karyar kare demokradiyya da hakkokin bil'Adama suka yi wa al'ummar na kada su fito wajen kada kuri'an....... Karin Bayani


 

Nasarorin Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran:
(Muhammad Awwal Bauchi)

Hakika nasarar da Juyin Juya Halin Musulunci na Iran karkashin jagorancin marigayi Ayatullah Imam Khumaini (r.a) ya samu a ranar 11 ga watan Fabrairun 1979 ya haifar da abubuwa da yawa da kuma tabbatar da wasu masu dama wadanda kafin hakan an rasa su ko kuma ma ana tunanin ba za su iya samuwa ba sakamakon jahilcin masu wannan tunani ko kuma kin gaskiyarsu saboda wasu manufofi na ta daban. Ko ba a fadi ba daga cikin irin nasarori da abubuwan da juyin ya tabbatar sun hada har da: tabbatar da rashin ingancin raba addini da siyasa, tabbatar da karfin addinin Musulunci da Shi'anci wajen iya gudanar da harkokin al'umma..... Karin Bayani


 

Gudummawar Zaben "Shaikh Ga Mista Bush:
(Muhammad Awwal Bauchi)

A daidai lokacin da 'shugaba' Bush da sauran 'yan tawagarsa na jam'iyyar 'Republican' suke cikin zullumin yiyuwar shan kaye a zaben shugaban kasar Amurka sakamakon rashin nasarar da suke fuskanta a kasashen Afghanistan da Iraki, ga kuma batun bacewar ton-ton na sinadarori masu fashewa a kasar Iraki, sannan kuma ga batun zaton da ake yi cewa za su yi magudi a zaben, kwatsam sai ga "Shaikh", da daman ake tsammanin faruwar hakan, ya fito ya share musu hawaye....... Karin Bayani


 

Shari'ar Saddam Husaini....Karshen Alewa Kasa:
(Muhammad Awwal Bauchi)

Masu iya magana dai sukan ce wai karshen alewa kasa, kuma wai in zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere don watakila nan gaba ka fada cikinsa. A yau Laraba ne ake sa ran jami'an Amurka za su mika tsohon shuganan mulkin kama karya ta Iraki Saddam Husaini tare da wasu jami'an tsohuwar gwamnatinsa guda 11 ga sabuwar gwamnatin Iraki, sannan kuma a gobe alhamis 1 ga watan Yuli ake sa ran za a gurfanar da su a gaban kuliya manta sabo don fuskantar irin ta'addancin da suka yi wa al'ummar Iraki....... Karin Bayani


 

28 Ga Yuni...Mika Mulki Ko Kuma Sabon Makirci:
(Muhammad Awwal Bauchi)

A ranar Litinin 28 ga watan Yunin nan ne jami'an Amurka suka ce sun mika madafan mulki ga al'ummar Iraki ko kuma dai a ce gwamnatin da suka zaba ko kuma wacce aka kafa bisa amincewarta, kwanaki biyu kafin lokacin da suka yi alkawarin yi. Duk da cewa dai da dama suna ganin wahala ce ta sa Amurkawan yarda su mika dan wannan kwarya-kwaryan mulki ga Irakawan saboda matsalolin da suke fuskanta....... Karin Bayani


 

Sayyid Khamene'i Salihin Magajin Imam Khumaini:
(Muhammad Awwal Bauchi)

Juyin Juya Halin Musulunci na Iran dai ya dogara ne a kan wasu rukunai guda uku da suka ba shi damar samun nasara da tsayawa da kafarsa har zuwa yau din nan, su ne kuwa Musulunci, al'umma da kuma jagoranci ko kuma jagora. Addinin Musulunci dai shi ne abin da juyin ya rike a matsayin tsari, al'umma kuma a matsayin masu ba da goyon baya, jagora kuwa a matsayin garkuwa kana mai shiryar da juyin da kuma kula da cewa abin da ake yi bai kauce daga tsarin da aka kafa shi a kai ba....... Karin Bayani


 

Imam Khumaini Da Duniyar Musulmi:
(Muhammad Awwal Bauchi)

Duk da cewa shekaru goma sha biyar kenan muke ciki na wafatin Marigayi Imam Khumaini, Mu'assasin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kana kuma Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci amma har ya zuwa yanzu al'ummar musulmi suna jin zafin wannan babban rashi da suka yi, to sai dai abin da ke faranta rai shi ne cewa har ya zuwa yanzu din kalamai da rubuce-rubucensa sun kasance abubuwan da suke shiryar da al'umma wajen samun nasara a wannan duniya da kuma samun kyakkyawan sakamako a rayuwarsu ta gobe....... Karin Bayani


 

Saudiyya...Hattara Daga Makircin Amurka Da H.K.Isra'ila:
(Muhammad Awwal Bauchi)

A halin da ake ciki dai kasar Saudiyya ta nuna kudurinta na fada da ta'addancin cikin gida wanda cikin shekaru aka dasa da kudin man fetur da ke shiga hannun wasu kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da ba sa amfani da hankali wajen ayyukansu, wadanda kuma ba su da wata alaka da addinin Musulunci, duk da kokarin da kafafen watsa labaran yammaci suke yi na alakanta su da addinin Musuluncin....... Karin Bayani





Bayani Kan Imam Khamene'i

Shi'a Imamiyya

Hannunka Mai Sanda

Ko Kun San?

Links

Sauran Abubuwa
Na Gama Tsara Wannan Shafin Ne A Ranar 25 Ga Watan Zil Hajji 1421, Wanda Yayi Daidai Da Ranar Da Aka Saukar Da Surar Al-Insan (wato ayar: ...Kuma Suna Ciyar Da Abinci, A Kan Suna Bukatarsa, Ga Matalauci Da Maraya Da Kamamme. (Suna cewa), Muna Ciyar Da Ku Ne Domin Neman Yardar Allah Kawai, Ba Mu Nufin Samun Wani Sakamako Daga Gare Ku, Kuma Ba Mu Nufin Godiya...Surar Insan Aya Ta 8-9), Akan Amirul Muminina, Aliyu bn Abi Talib, Fatima al-Zahra, Hasan Da Husaini (a.s.). Nayi Hakan Ne Kuwa Don Neman Izininsu Da Kuma Yin Tawassuli Da Su, Ko Za Su Ja Hannayena Zuwa Ga Ubangijinsu A Ranar Da Babu Wani Mai Ceto Sai Su Ko Kuma Da Izininsu.

Muhammad Awwal Bauchi ne ya tsara da gina wannan shafi. Kofa ta a bude take bisa duk wasu shawarwari da ra'ayoyinku kan wannan shafi.
Kuna iya aiko da ra'ayi da shawarwarinku ta adreshi na kamar haka: awwalbauchi@hotmail.com