Sayyid Khamene'i Salihin Magajin Imam Khumaini:
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Jagora Imam Khamene'i - Yayin Da Yake Gaida Mutane

Juyin Juya Halin Musulunci na Iran dai ya dogara ne a kan wasu rukunai guda uku da suka ba shi damar samun nasara da tsayawa da kafarsa har zuwa yau din nan, su ne kuwa Musulunci, al'umma da kuma jagoranci ko kuma jagora. Addinin Musulunci dai shi ne abin da juyin ya rike a matsayin tsari, al'umma kuma a matsayin masu ba da goyon baya, jagora kuwa a matsayin garkuwa kana mai shiryar da juyin da kuma kula da cewa abin da ake yi bai kauce daga tsarin da aka kafa shi a kai ba. Don haka ne al'ummar Iran da ma na sauran kasashe, musamman makiya suke ba da muhimmanci da kuma kula da yanayin wannan jagora saboda irin matsayin da yake da shi wajen ci gaban juyin da kuma dawwamarsa. Tun kusan karshe-karshen rayuwar marigayi Imam Khumaini (r.a), wanda shi ne Mu'assasin wannan juyi, al'umma (masoya da makiya) suka shiga cikin damuwa da zullumin cewa wane ne zai gaje shi idan ya rasu. Su dai masoya damuwarsu ita ce wane ne zai iya ci gaba da wannan aiki na Imam wajen ganin juyin bai fadi ba, a bangare guda su kuma makiya abin da suke fata shi ne gaggawa rasuwar Imam din don samun damar cimma burorinsu da daman suke ganin Imam din ne ya toshe musu hanyar da za su iya gare su. A takaice dai tambayar da take ta yawo ita ce, wane ne zai zama jagora bayan Imam?

To sai dai ba a dau lokaci mai tsawo ba daga rasuwar Imam, sai ga shi an amsa wannan tambaya da kwantar da hankalin masoya, su kuwa makiya aka dada kara musu damuwa a zuci. Wannan amsa kuwa ita ce, zaben da 'yan Majalisar Kwararru ta Zaben Jagora suka yi wa Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i a matsayin sabon jagora. Ko ba a fadi ba wannan zabe da aka yi zabe ne da ya dace saboda irin siffofin da shi Ayatullah Khamene'i yake da shi ga kuma kusancin da yake da shi da Imam har ma an ruwaito shi (Imam) a wasu lokuta yana cewa: Shi (Ayatullah Khamene'i) mutum ne da ya cancanci shugabanci. Wannan zabe dai ya sa hankulan mutane sun kwanta daga fargaban da suke ciki, su kuwa makiya an kara musu damuwa da yanke kauna daga cimma burorinsu. Wannan batu dai ya tuna wa kowa fadin Allah Madaukakin Sarki, lokacin da Manzon Allah (s.aw.a) ya zabi Amiral Muminina Ali (a.s) a matsayin halifansa a Ghadir Khum bayan dakon mutuwarsa da kafirai suka kasance suna yi, cewa: ( اليوم يئِسَ الَذين كفروا منْ دينِكمْ فلاَتخشوهُمْ واخْشَوْني ) "A yau wadanda suka kafirta sun yanke kauna daga addininku, saboda haka kada ku ji tsoronsu, ku ji tsoroNa". (Suratul Ma'ida: 5:3).

A hakikanin gaskiya dai ayyuka da siffofin da Ayatullah Khamene'i ya mallaka a rayuwarsa ta yau da kullum ko kuma tun lokacin da ya karbi wannan babban nauyi na jagoranci, babu wani kokwanto kan cewa lalle shi ne magaji na asali kana kuma mai cike gurbin da Marigayi Imam Khumaini (r.a) ya bari. Hakan kuwa saboda wasu siffofi ne da yake da su wadanda ya koyo su daga wajen Imam sannan kuma ya sanya suka zamanto wani bangare na rayuwarsa ta yau da kullum, sannan kuma yana ganin kansa ne a matsayin garkuwa kana mai gadin madaukakin tafarkin Juyin Juya Halin Musulunci da kuma Marigayi Imam, kuma ya tabbatar da hakan a aikace ba wai kawai a fatar baki ba. Daya daga cikin abubuwan da suke nuni da hakan shi ne irin rikon da ya yi ga batun 'yancin kasar Iran da kuma rashin mika wuya ga duk wani karfi na duniya musamman ma a halin da muke ciki da kurayen duniya ma'abuta girman kai suka baza faratunsu don cinye al'ummomin duniya musamman wadanda suka ki mika musu wuya. Wani abu kuma shi ne tsayin dakan da Imam Khamene'in ya yi wajen goyon bayan al'ummomin duniya da ake zalunta kamar yadda Imam Khumaini ya kasance yana yi. Jagora Imam Khamene'i - Yayin Da Yake Takarda Kama Aikin Shugabancin Kasa A Wajen Imam (r.a)

Jagora Imam Khamene'i, kamar Imam Khumaini, yana ganin goyon bayan marasa galihu da wadanda ake zalunta a matsayin wani nauyi na addini da 'yan'Adamtaka, don haka ne ya kasance cikin nuna goyon baya ga al'ummomin da suke karkashin cutarwa da zalunci na makiya, misalinsu kuwa shi ne kasar Palastinu da Iraki cikin 'yan kwanakin nan, a bangare guda kuma da yin Allah wadai da azzaluman da suke zaluntar al'umma, Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila a kan gaba, bugu da kari kan kira da a fuskance su kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar sannan kuma Imam Khumaini (r.a) ya jadddada.

Baya ga wadannan siffofi na jagoranci da shiryar da al'umma da Ayatullah Khamene'i ya mallaka, akwai kuma wasu siffofin na kyawawan dabi'u da yake da su wadanda su ma abin a kula da su ne. Daya daga cikin dabi'un Jagora Khamene'i da za su fara janyo hankula zuwa gare shi, shi ne rayuwa mai sauki da yake yi a gidansa duk kuwa da matsayin da yake da shi. Wadanda suke kusa da shi sun tabbatar da cewa rayuwarsa ba ta dara irin ta talakawan Iran ba, idan ma ba ta gaza ba, don kuwa yana raye ne a gidan da bai taka kara ya karya ba, haka nan ma kayan da ke cikin gidan, irin wannan rayuwa ta kasance abin ban al'ajabi ga duk wadanda suka kai masa ziyara musamman ma wadanda suka zo daga kasashen waje.

Daga cikin wadanda suka kasance na kurkusa da Jagoran dai akwai marigayi Sayyid Ahmad Khumaini, dan Marigayi Imam, yayin da yake Magana kan rayuwar Ayatullah Khamene'i yana cewa:

"Har abada, ba za ka ga an kawo nau'i sama da guda na abinci ba a inda Jagora da iyalansa suke cin abinci, a hakikanin gaskiya rayuwarsa rayuwa ce mafi sauki".

Har ila yau, dan Sayyid Ahmad din wato Hujjatul Islam Sayyid Hasan Ahmad Khumaini, a wata ziyara da muka kai masa, ya bayyana mana irin rayuwar Sayyid Khamene'i a matsayin rayuwa ce mai sauki ta irin kowani talaka sabanin abin da ta yiyu wani yake zato na cewa yana rayuwa ne cikin jin dadi da annashuwa yana mai cewa yana fadin hakan ne a matsayinsa na wanda yake shiga cikin gidan Jagoran ba wai an gaya masa ba ne.

Baya ga hakan kuma, Ayatullah Khamene'i ya kasance madaukakin mutum ne, don kuwa wannan siffa ta daukaka da ikhlasi na daga cikin sharadin jagoranci a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wato dole ne Jagora ya kasance mai madaukakiuar siffa, mai mika kai ga Allah Madaukakin Sarki kama mai aiki dominSa don ya samu damar gudanar da aikinsa na jagorantar al'umma. Neman kusanci da Ubangiji dai da suka hada da salloli, azumi, karatun Alkur'ani mai girma da dai sauransu na daga cikin tsare-tsare na yau da kullum na Jagoran da ba ba ya taba wasa da su. Dangane da hakan an jiyo wani na kurkusa da shi yana cewa:

"Duk da yawan ayyukan da ya ke da shi a kowace rana, amma cikin dare Jagora ya kan tashi don ibada da salloli. Wannan dabi'a dai ita ce ta ba shi damar ci gaba da yin hidima wa al'umma da dukkan karfi, sannan da kuma tsayawa kyam a gaban azzalumai".

Wata siffar kuma da Jagoran ya mallaka ita ce tsantsaini cikin Baitul Malin musulmi, wannan siffa ce ta sanya shi a kowani lokaci ya kan kira jami'an gwamnati da kada su sanya idanuwansu akan Baitul Malin da kuma nesantar abin da ke ciki. Don cimma wannan manufa ta kiyaye dukiyar al'umma ne ma cikin watannin da suka wuce ya ba da umarni ga sassa uku na gwamnati (bangaren gudanarwa (gwamnati), majalisa da ma'aikatar shari'a) musamman ma dai Ma'aikatar Shari'ar da ta gudanar da bincike kan jami'ai da kuma nuna ba sani ba sabo ga duk wanda aka samu ya ci dukiyar al'umma.

Daya daga cikin siffofin jagoranci a tsarin Musulunci na Iran da dole ne duk wani wanda zai zamanto jagora ya mallake su shi ne masaniyya kan ilmummuka da dokokin Musulunci. Don haka, Ayatullah Khamene'i, a matsayinsa na jagora, ya kasance mutum ne masani da ya mallaki masaniyyar dukkan ilmummukan da ake bukata wajen hawa wannan matsayi na jagoranci. Na farko dai ga shi marja'i ne da miliyoyin al'umma a duniya suke masa takalidi (yin koyi da shi), sannan kuma duk da ayyukan da yake da su a kowace rana, amma yana karantar da dalibai ( Bahasul Kharij) da dai sauran ilmummuka. Baya ga masaniyya ta fikihu, Imam Khamene'i kuma masani ne a bangaren tarihin Musulunci, falsafa, Irfani, tafsiri da dai sauransu, irin wannan yanayi ne ya ba shi damar fitar da ra'ayin Musulunci a bangarori daban-daban na rayuwa musamman ma a wannan zamani da muke ciki.

Sabanin sauran shuwagabanni, Ayatullah Khamene'i, duk da irin ayyukan da yake da su, amma ba su hana shi damuwa da matsalolin al'umma ba da kuma kokarin magance su. Daya daga cikin hanyoyin da yake bi wajen gano matsalolin al'umma, baya ga ziyara ta sirri da yake kaiwa ma'aikatu na gwamnati da sauran wajaje na al'umma, ita ce ta hanyar rahotannin da yake samu daga bangarori daban-daban na kasa, a wasu lokuta kuma ya kan san halin da ake ciki ne ta hanyar sauraren koke-koken al'umma da suke kai masa ziyara gidansa akai-akai da kuma tattaunawa da shi, baya ga haka sai kuma ta hanyar ziyarar da shi kansa yake kai wa gidajen mutane da unguwanni musamman ma na marasa abin hannu don ganin irin halin da suke ciki.

Daya daga cikin bangarorin da Jagoran ya fi ba su muhimmanci shi ne bangaren matasa. Jagora Khamene'i dai ya kasance mutum ne mai ba da muhimmancin gaske ga matsalolin matasa, saboda imanin da yake da shi cewa su ne manyan gobe. Don haka yake ba da kulawa ta musamman don magance matsalolinsu da suka hada da rashin aikin yi, aure, karatu da dai sauransu. A kowace shekara, jagora Khamene'i ya kan yi aure da ba da abin da ake bukata ga dubban matasa wadanda ba su da abin yin aure. Jagoran ya kan gano irin matsalolin matasan ne ta hanyar ganawa da su a lokuta daban-daban a gidansa baya ga kai ziyara cibiyoyin matasa da kuma jami'oi da yake yi don sanin matsalolin da suke ciki da kuma hanyoyin da za a bunkasa irin falalar da Ubangiji ya yi musu don ci gabantar da kasa da dai sauransu. A irin wadannan ganawa, baya ga jawabi da shiryar da matasan kan dabi'u na kwarai da dai sauransu, Jagoran ya kan saurari ra'ayuyyukan matasan da kuma koke-kokensu dangane da yadda ake gudanar da mulki da dai sauransu. A lokuta da dama wasiyyoyin da Jagoran ya kan yi wa matasan sun hada har da kokari wajen neman ilmi da kuma ba da himma wajen harkokin wasanni.

Wadannan siffofi dai suna daga cikin siffofin jagora a tsarin Musulunci na Iran, don haka ne masana suke ganin Ayatullah Khamene'i a matsayin mutumin da ya fi dacewa ya gaji Imam Khumaini a wannan matsayi na jagorantar al'umma da kuma shiryar da su bugu da kari kan kare su daga sharri da makirce-makircen makiya.