Wafatin Ummul Muminina Khadijah (a.s)

Ummul Muminina Khadijah bint Khuwailid, matar Ma'aikin Allah (s) ta rasu ne a ran 10 ga watan Ramalana shekara ta goma da aiko Ma'aiki (s), wato shekara uku kenan kafin hijira, a lokacin kuwa tana da shekaru 65 a duniya.

Kafin rasuwarta dai, Khadijah ta ba da gudummawa mai girman gaske wajen kare Ma'aikin Allah (s) da kuma ci gabantar da Musulunci a lokacin da yake cikin mawuyacin hali. Saboda irin wannan gagarumar gudummawa da Nana Khadijan ta bayar ne aka ruwaito Manzon Allah (s) yana cewa: 'Ba don kariya ta Abu Talib ba, da kuma dukiyar Khadijah da kuma takobin Ali ba, da wannan addini bai tsaya ba da kafarsa ba.

Wannan rasuwa ta Khadijah dai ya kasance babban rashi ga Ma'aikin Allah da kuma 'yarsa Fatima (a.s) inda har tazo tana kuka tana ce Baban nata (s) ina mahaifiyata, nan take sai Mala'ika Jibril (a.s) ya sauko ya ce wa Annabi (s): "Ka ce wa Fatima cewa Allah Madaukakin Sarki Ya gina wa mahaifiyarta gida a aljanna da zinare....".

Hakan kuma saboda irin wannan babban musiba da ta sami Manzon Allah (s) na wannan rashi na Khadijah da kuma rasuwar baffansa kuma mai kare shi Abu Talib (a.s), ya sa ya kira wannan shekara (da suka rasu a cikinta) da "Shekarar Bakin Ciki".

  • Wace Ce Khadijah
To yanzu bari mu yi dubi kan wace ce Khadijah?

Ita ce dai Khadijah bint Khuwailid bn Asad bn Abdul Uzza bn Qusay, tana daga cikin manyan matan Kuraishawa kana kuma wacce ta fi su kyau, tun kafin Musulunci ma ana kiranta da suna at-Tahira (tsarkakakkiya) saboda irin kyawawan dabi'unta, kuma ana kiranta da 'Shugaban (matan) Kuraishawa.

Irin wadannan kyawawan halaye nata da kuma irin daukakan da take da shi ya sa wasu daga cikin manyan Kuraishawa, irin su Utbah bn Abi Mu'it, Abu Jahl, Abu Sufyan, da dai sauransu, suka bukaci aurenta da kuma nuna mata kudi, to amma dai taki ta zabi Manzon Allah (s) saboda halayensa na kwarai da ta gani.

To kamar yadda muka fadi Khadijah mace ce mai dukiya, kana kuma tana son wanda zai kula mata da wannan dukiya ta ta cikin aminci ba tare da cuta ba, don haka sai ta bukaci Manzon Allah (s), wanda daman tun zamanin Jahiliyya mutanen Makka suna kiransa "As-Sadikul Amin, da ya kula mata da wannan dukiya nata. Da farko dai ya ki yarda, to amma daga baya ya amince da hakan.

Bayan wannan yarda da Manzon Allah (s) ya yi da wannan bukata ta Khadijan, sai suka fita kasuwanci tare da wani bawan Khadijan mai suna Maisara. A yayin wannan fatauci dai an sami riba mai yawan gaske, hakan kuwa saboda albarkar da ke tare da Ma'aikin ne da kuma gaskiyarsa. To bayan dawowarsu, da kuma irin labarin da wannan bawa na Khadijah ya bata dangane da irin kyawawan halaye na Manzon Allah (s) nan take sai so da kaunarsa ta cika zuciyar Khadijah, inda ta bukaci in ya yarda ya aure ta.
  • Auren Manzon Allah (s) da Khadijah (a.s):
An ruwaito daga Ammar bn Yasir (r.a) yana cewa: "Ni nafi kowa sanin auren Manzon Allah (s) da Khadijah bint Khuwailid; don na kasance abokin Ma'aiki (s). Wata rana muna tafiya tare da Manzon Allah (s) tsakanin Safa da Marwa sai ga Khadijah bint Khuwailid tare da 'yar'uwarta Hala. Lokacin da suka ga Manzon Allah (s) sai Hala ta ja ni gefe ta ce min: 'Ya Ammar! Abokinka ba shi bukatuwa (da auren) Khadijah?
Sai na ce: 'Wallahi ban sani ba. Sai na koma na gaya masa.
Sai ya ce min: "Koma ka sa mana lokacin da za mu je mu gana da ita....sai kuwa na koma na aikata hakan (wato muka sa rana).
Da ranar ta zo.....sai Manzon Allah (s) ya zo da baffanninsa karkashin jagorancin Abu Talib, inda ya karbi aurenta a hannun baffanta Amru bn Asad, kasantuwan mahaifinta, Khuwailid bn Asad ya rasu.


A takaice dai haka auren Manzon Allah (s) da Khadijah (a.s) ya kasance.
  • Matsayin Khadijah A Wajen Manzon Allah (s):
Bayan gama bukuwan aure, sai Manzon Allah (s) ya koma gidan Khadijah da zama, wannan gida da ke da dimbin tarihi wajen ci gabantar da musulunci da kuma taimakon marasa galihu.

A yayin zamansu dai, Khadijah ta kasance mace mai tsananin biyayya ga mijinta da kuma taimaka masa a dukkan bangarorin rayuwarsa, kamar yadda shi ma ya kasance hakan tare da ita. A lokacin da aka aiko shi a matsayin annabi, ita ce mace ta farko da ta fara imani da shi, ta karbi wannan kira nasa, ta ba da dukkan abin da ta mallaka don Allah da kuma ci gabantar da wannan addini.

Babu makawa, dole ne Manzon Allah (s) ya saka mata saboda irin wannan hidima da ta yi masa da kuma addinin Allah, don haka ya kasance mai tsananin sonta, girmama ta lokacin tana raye da ma bayan rasuwarta (a.s), daboda matsayin da take da shi a cikin zuciyarsa.

An ruwaito cewa, bayan rasuwarta, a duk lokacin da ya yanka wani abin yanka, ya kan dauki wani bangare na naman ya ce: "Ku aika wannan wa kawayen Khadijah'. An ce wata rana A'isha, matar Manzon Allah, ta tambaye shi me yasa yake haka: sai ya ce mata: "Saboda ina sonta".

Haka nan ma an ruwaito cewa wata mace ta zo wajen Manzon Allah (s), a lokacin yana dakin A'isha. Nan take ya tashi ya karbe ta hannu bibbiyu ya gaggauta biya mata bukatan da ta zo nema. Wannan lamari ya ba wa A'isha mamaki, sai ta tambaye shi dalilin hakan, sai ya ce mata: "Ta kasance tana zuwa gurinmu lokacin rayuwar Khadijah".

Har ila yau kuma an ruwaito A'ishan dai tana cewa: 'Wata rana Manzon Allah (s) zai fita daga gida, sai ya tuna da Khadijah, ya fadi wasu kalmomi na girmamawa gare ta. To amma sai na gagara rike kai na sai na ce masa; 'Ita dai ba wani abu ba ne face tsohuwar mace, kuma a halin yanzu Allah ya musanya maka wadanda suka fi ta'.
Nan take Manzon Allah (s) ya mayar mata da martani, cikin fushi yana cewa: "Lallai ba haka ba ne...lalle ban samu wadanda suka fi ta ba. Don kuwa ita ce ta yarda da annabcina a lokacin da kowa ya kyale ni. Ta ba ni dukkan dukiyarta a lokaci mafi tsanani (na bukatuwa da su). Kuma Allah Ya ba ni zuriya ta hannunta, alhali kuwa ya haramta min daga wasunta".

Barka gare ki Ya Khadijah, barka gare ki Ya ke wacce Allah Yake sonki kuma Ya kuma miki alkawarin dawwama cikin ni'iman (aljanna). Don an ruwaito cewa Mala'ika Jibril (a.s) ya zo wajen Manzon Allah (s) ya ce masa; "Ya Rasulallah! Ga Khadijah nan za ta zo gurinka da kwarya na na abinci, idan ta zo ka isar da gaisuwar Ubangijinta gare ta da kuma tawa gaisuwar, ka kuma yi mata bushara da gida a aljanna da aka gina shi da zinare....."

A saboda haka ne Manzon Allah (s) ya ce:
"Mafiya daukakan matan aljanna su ne: Khadijah bint Khuwailid,Fatima bint Muhammad, Maryam bint Imran, Asiya bint Muzahim, (matar Fir'auna)