Shahadar Amirul Muminin Imam Ali (a.s)

Bayan saran da la'anannen Allah Abdurrahman bn Muljam ya yi wa Imam Ali (a.s) da takobi mai guba alhali yana salla, da kuma kame shi Abdurrahman din a lokacin da ya yi kokarin gudu, sai aka dawo da Amirul Muminin gida, inda ya ci gaba da zama cikin wannan hali na zafin saran da aka masa har na tsawon kwanaki uku.

Imam (a.s) ya saura yana fama da jinya har na tsawon kwanaki uku har zuwa lokacin da ya yi shahada a ranar 21 ga watan Ramalana mai albarka, shekara ta 40 bayan hijira. A cikin wadannan kwanakin ya mika akalar Imamanci ga dansa Hasan a bayan shi, don ya dauki dawainiyar ja-gorancin al'umma, ya kuma ci gaba da tafiyar da Imamanci a bayan shi.

An kashe Imam (a.s) a lokacin yana mafificin lokaci da ya ke tsaye a gaban Allah a cikin sallarsa mai cike da kaskantar da ki ga Allah Madaukaki; a cikin mafi daukakar ranaku, domin yana dauke da azumin watan Ramadhan; a lokacin yana cikin aiwatar da mafi girman taklifin Musulunci, wato yana kan hanyarsa ta jihadi; kamar yadda ya kasance a wani lungunan Allah Madaukaki kuma mafi tsarkin su (wato masallancin Kufa).

Wannan aika-aika ba wai ta nufi wani mutum ne kamar sauran mutane ba; a'a ta nufi shugabancin Musulunci ne bayan Annabi (s.a.w.a), ta kuma nufi kashe sako, tarihi, wayewa da al'umma ne baki daya, mai ci-gaba da tafiyarsa da aikinsa.

Da wannan al'ummar Musulmi ta yi hasarar tafiyarta da wayewarta, tana kallo ta yi rashin mafi kyawun daman da take da shi bayan Annabi (s.a.w.a).

A tsawon kwanaki nan uku kamar yadda ya kasance a duk tsawon rayuwarsa Imam (a.s) ya kasance cikin ambaton Allah da yabonsa da yarda da hukucinsa da mika wuya ga horonsa. Ya rika fitar da wasiyyoyi daya na bin daya, yana mai shiryarwa zuwa ga alheri, mai shiryawa zuwa ga aikin kirki, mai iyakance tafarkin shirya, mai bayyana hanyar tsira, mai kira zuwa tsayar da dokokin Allah Madaukaki da kiyaye su. Daga cikin wasiyyoyisa ga 'ya'yansa da sauran dukkan mutane akwai wanda muka kawo a bangaren ranar da aka sare shi, mai so yana iya komawa don ganinta.

Haka karshen wannan babban mutum ya kasance mai kona rai; hakika rashin shi ya kasance mafi girman hasara ga wannan al'umma bayan Annabi (s.a.w.a); domin al'umma ta rasa tsaikon gwarzontaka da kokari da hikima, kuma cikakken abin koyi wajen tsarkaka, gudun duniya, ilimi da fahimtar addini. Shi ne wanda Manzon Allah (s.a.w.a), dangane da shi, ya ce, shi:
"Ali na tare da gaskiya, kuma gaskiya na tare da Ali"

Amincin Allah Ya tabbata a gare ka Ya Amirul Muminina, Ranar da aka haife ka, da ranar da ka yi shahada da kuma ranar da za a tashe ka kana rayayye. Kaiconmu da mun kasance tare da kai (a wancan ranan)da mun amfana amfanuwa.