Daren Da Aka Sari Imam Ali (a.s) da Takobi Mai Guba

Bayan yarjejeniyar yaudara da aka yi a yakin Siffin abin da ake kira Tahkim tsakanin Amr bn Aas da Abu Musa al-Ash'ari, wasu kungiya daga cikin musulmi sun fandare wa Amirul Muminina (a.s) wanda ake kiransu Khawarij,duk da cewa Amirul Muminin din ya yi kokarin nusantar da su kan wannan tafarki da suka dauka da kuma ba su lokaci ko sa tuba amma dai sun ki yin haka, sai ma dai suka dinga tara sojoji don yakansa da kuma halalta jininsa, abin da ya haifar da yaki a tsakaninsu, yakin da ake kira da Yakin Nahrawan.

To bayan wannan yaki da kuma nasarar da dakarun gaskiya karkashin jagorancin Aliyu bn Abi Talib suka samu akan Khawarijawan,sai wasu daga cikinsu suka yi taro a Makka, suka tsayar cewa za su kashe Amirul Muminina (a.s), Mu'awiyyah bn Abi Sufyan da kuma Amr bn al-Aas, wadanda a ganinsu su ne suka hana ruwa gudu a duniyar musulmi.

Don haka sai suka tsayar cewa Abdurrahman bn Muljam (La'anar Allah Ta Tabbata a gare shi) shi ne zai kashe Amirul Muminina (a.s). Don haka sai ya fara shiri ya nufi Kufa, inda helkwatar Amirul Muminina take don aikata wannan danyen aiki nasa. Kuma ya tsara zai sari Amirul Muminin din ne a ya yin da yake salla.

Don haka tun a daren wannan rana ta 19 ga watan Ramalana shekara ta 40 bayan hijira sai ya nufi masallacin Kufa yana mai dakon isowar Amirul Muminina don ba da sallar asubahi.

To daman tun da jimawa Amirul Muminina (a.s) ya bayyana shahadar tasa a wannan rana, don daman Manzon Allah (s) ya masa bayanin hakan, don haka a wannan ranar ma da zai fita sallar asubahi sai ya ce wa 'ya'yayensa (Imam Hasan da Husaini) da su zauna a gida, kada su biyo shi masallaci kamar yadda suka saba. An ruwaito cewa lokacin da ya shirya zai fita hatta dabbobin da suke gidan sai da suka ta kuka, koda masu aikin gidan suka yi kokarin hana su, sai Amirul Muminina ya ce su barsu ba komai suke yi ba face suna juyayin mutuwarsa ne.

Koda ya isa masallaci ya kira salla, kana kuma ya fara jagorancin mutane a sallar, sai wannan la'anannen Allah (Abdurrahman bn Muljam) wanda da man ya samu wuri a sahun gaba sai ya taso ya sari Amirul Muminina a kansa, sara mai tsanani da takobinsa mai tsananin guba a jiki. Nan take Amirul Muminina ya fadi cikin jini, kamar yadda da man Manzon Allah (s) ya gaya masa wata cewa: "Ya Ali! An nuna min yadda wannan gemu naka zai jika da jinin kanka".

Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!, kalmar farko da ta fara fita a bakin Amirul Muminina (a.s) ita ce Fuztu wa Rabbil Ka'aba", wallahi na sami babban rabo.

Nan take dai sahabban Amirul Muminin suka kame wannan la'anannen Allah, yayin da yake kokarin gudu bayan ya aikata wannan danyen aiki, a ka kawo shi gaban Amirul Muminin. Koda ya ga irin tsananin daurin da aka yi wa Abdurrahman din, sai ya bukaci da a sassauta masa kuma a yi masa mu'amala mai kyau. Ganin irin wannan dabi'a ta kwarai, sai ya (Abdurrahman bn Muljam) ya fara kuka, sai Amirul Muminin ya ce masa "Ai lokaci ya kure maka na tuba, don ka riga da ka aikata abin da ka aikata....".

Daga nan sai Amirul Muminin ya ba da umurnin cewa kada a kuntata wa wannan makashi nasa, kada a azabtar da shi, kada a lalata gawarsa bayan kashe shi, kada a kuntata wa iyalansa saboda wannan aiki da ya yi, haka nan kuma kada a ce za a kwace dukiyansa. Allahu Akbar! adalcin Amirul Muminina ba wai kawai ya tsaya ga masoyansa ba ne hatta ma ga makiyansa.

Bayan haka sai aka dauki Amirul Muminina (a.s) aka kai shi gida, inda ya ci gaba da rayuwa cikin wannan tsanani na ciwo har lokacin da Allah Ya karbi ransa yana a matsayin shahidi. Kafin hakan kuwa ya ci gaba da amsa tambayoyi da kuma yin wasiyoyi daban-daban ga mabiyansa da kuma 'ya'yansa.

Bari mu kawo wasiyyarsa ta karshe ga 'ya'yansa (Hasan da Husain) da kuma sauran iyalansa da kuma al'umman musulmi.

Wasiyyar Karshe Ta Amirul Muminin (a.s):

Ina muku wasicci da tsoron Allah da kuma shawartarku da kada ku rusuna ga (jin dadin) duniya ko da kuwa tana binku, sannan kuma kada ku yi bakin ciki akan wani abu na duniya da aka hana ku. Ku fadi gaskiya da kuma yin aiki don lada. Sannan ku kasance masu tsanani ga azzalumai, kana masu taimakon wanda aka zalunta.

Ina muku wasicci, da kuma dukkan 'ya'yayena da iyalaina da dukkan wanda rubutuna ya isa gare shi, da tsoron Allah da tsara al'amurranku da kuma kyautata alaka tsakaninku, don kuwa na ji kakanku (Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Kyautata tsakani ya fi salla da azumi".

Ina hada ku da Allah cikin al'amarin marayu, kada ku bari su shiga cikin wahala, sannan kada a cutar da su a gabanku.
Ina hada ku da Allah cikin al'amarin makwabtanku, don kuwa sun kasance wasiyyar Annabinku. Ya kasance yana yawan magana akansu har sai da muka tsammanci zai ba su wani sashi na gado.

Ina hada ku da Allah cikin lamarin Al-Kur'ani, kada ku bari waninku ya wuce gabanku wajen aiki da shi.

Ina hada ku da Allah cikin lamarin salla, don kuwa ita ce jigon addininku.

Ina hada ku Allah dangane da Dakin Ubangijinku (Ka'aba), kada ku kaurace masa matukar dai kuna raye, don kuwa idan kuka bar shi ba za ku tsira ba.

Ina hada ku da Allah kan jihadi saboda Allah da dukiyoyinku, kawukanku da harsunanku.

(Ina) gargadinku da kiyaye zumunci da biyan bukatun al'umma, sannan kuma ku nisanci nesantar juna da kuma yanke zumunci. Kada ku bar umurni da ayyukan alheri da kuma hani da munana, don sai mafiya sharrin cikinku su doru a kanku, kuma ku yi addu'a a ki karba.
Daga nan sai ya ce:
Ya ku 'ya'yan Abdul Mutallib, ba na kaunar in ganku kuna zubar da jinin musulmim kuna masu cewa: "an kashe Amirul Muminina". Ku kula kada ku kashe wani saboda ni in ba wanda ya kashe ni ba.

Ku hakura idan har na cika daga wannan sara da ya yi min, to ku sare shi kamar yadda ya sare ni, amma kada ku lalata jikinsa (gabobinsa), don na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: Ku guji lalata jiki koda kuwa jikin mahaukacin kare ne.

Amincin Allah Ya tabbata a gare ka Ya Amirul Muminina, Ranar da aka haife ka, da ranar da ka yi shahada da kuma ranar da za a tashe ka kana rayayye. Kaiconmu da mun kasance tare da kai (a wancan ranan)da mun amfana amfanuwa.