Gabatarwar Mai Shafi (Muhammad Awwal Bauchi)

 

 

 
Gabartarwar Mai Shafi
(Muhammad Awwal Bauchi)

________________________

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Muhammad Awwal Bauchi - Yayin Gudanar Da Bincike Kan Wani Lamari

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, Ubangijin talikai gaba daya, Wanda Ya halicce mu daga laka kana Ya tsara mu cikakken tsari kana kuma Ya fifita mu sama da dukkan halittu, sannan kuma ya arzurta mu da hankali don mu yi amfani da shi wajen banbance gaskiya da karya, sannan kuma don dada shiryar da mu Ya aiko mana Annabawa da Manzanni don su nuna mana hanya madaidaiciya kana kuma su kare mu daga sharrin Shaidan la'ananne, kana kuma suka shiyar da mu kan cewa mu bauta wa Allah Shi kadai da kuma riko da madaidaiciyar tafarki ta hanyar fahimta da kuma yarda, da kuma nesantar da mu da zama " 'yan amshin shatan" iyaye da kakanni wadanda suka ka riki wani tafarki ba tare da wata cikakkiyar hujja ba. Sannan tsira da amincinSa su tabbata ga Annabin rahama, cikamakin annabawa kana kuma Shugaban Manzanni, wanda yazo mana da shiriya da kuma rahama, mataimakin wadanda aka zalunta da kuma raunana, Shugabanmu Annabi Muhammadu dan Abdullahi (s) tare da tsarkakan Mutanen gidansa, wadanda Allah Ta'ala Ya zabe su su zama taurari masu shiryarwa da kuma haskaka hanya ga dukkan muminai kana kuma Ya wajabta soyayya da kuma kaunarsu ga dukkan muminai, da zababbun sahabbansa wadanda suka kasance tare da shi kana kuma suka taimaka masa tun daga farko har karshe ba tare da sun juya da baya ba, da kuma dukkan mabiyansu wadanda suke farin ciki da farin cikinsu kana kuma suke bakin ciki da bakin cikinsu, suke abokantaka da abokansu kana kuma suke gaba da makiyansu.

Bayan haka...., hakika hakkin Manzon Allah akan mabiyansa hakki ne mai girman gaske, koda yake saninsa da kuma kula da shi yana bambanta tsakanin mutane, lalle babu shakka kan cewa sonsa shi ne akan gaban wadannan hakkoki, don kuwa shi ne matakin farko na riko da abubuwan da ya bari, koyi da sunnansa, raya al'amurransa da kuma hakikanin binsa. Domin kuwa matukar ba'a samu kauna ta hakika ba, to babu yadda bi da kuma sadaukarwa zai tabbata. A don haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ke cewa:"Dayanku baya kasancewa mumini har sai na kasance abin soyuwa gare shi sama da kansa, mahaifinsa, dansa da kuma dukkan mutane".

Hakika sonsa (s.a.w.a.) reshe ne na son Ubangiji, Madaukakin Sarki, kuma dukkansu biyun sun kasance matakan farko ne na imani. Bugu da kari kuma wannan so nasa (s.a.w.a.) yana wajabta so da kauna ga makusantansa masu riko da amanarsa da kuma isar da sakonsa, don kuwa da haka ne wannan silsilar kauna ta kan cika, a duk lokacin da aka rasa ta kuwa, to babu wata ma'ana ga son Allah da kuma son ManzonSa, don haka aka ruwaito shi (s.a.w.a.) yana cewa:"Ku so Allah saboda abin da ya ciyar da ku na daga ni'imominSa, ku so ni saboda son Allah, kana kuma ku so Ahlubaitina saboda so na".

A saboda haka ne wannan nau'i na kauna ga Allah, ga ManzonSa da kuma mutanen gidan annabinSa ya kasance wani al'amari mai girman gaske cikin rayuwar daidaiku da kuma a jama'ance, kuma ya kasance wani mabudi ga alakar daidaiku da kuma al'umance da koyarwar Ubangiji, kamar yadda Allah da ManzonSa suka shiryar da mu kuma suka umurce mu da hakan, don kuwa sune taskokin ilminSa, masu kiyaye amanoninSa, mafifita akan sauran al'umma ta ko ta wani dangare.

To don haka ne na tsara wannan shafi don amfanin dukkan al'umma gaba daya, musamman ma masu magana da harshen Hausa, don sanin wani abu daga cikin koyarwar Ahlulbaitin Manzon Allah (a.s), wadanda su ne "Jirgin Annabi Nuhu" wanda ya rike su ya tsira wanda kuwa yayi watsi da su ya halaka.

Koda yake dai abinda muka rubuta a ciki bai kai ko cikin cokali na koyarwa Ahlulbaiti (a.s.) ba, to amma dai duk da haka, watakila dalibai iri na zasu iya amfana da dan abin da ya sawwaka daga cikin abin dake cikin shafin. Koda yake akwai wasu wurare da bamu gama aiki a kansu ba, to amma saboda shawarar da wasu 'yan uwa da abokan arziki suka bayar na gaggauta sanya shafin cikin "Internet" don amfani masu karatu, yasa na sanya shi, to amma da yardar Allah zamu dinga kara abubuwan da suka saura. Don haka sai mai karatu ya dinga leka wa don ganin chanje-chanjen da aka samu.

Saboda la'akari da kokari da kuma taimaka min da wasu 'yan uwa na suka yi wajen tsara wannan shafi, ta hanyar bada shawarwari da dai makamantansu, don haka ba zan rufe wannan gabatarwa ba har sai na gode musu da kuma rokon Ubangiji Tabaraka wa Ta'ala da Ya saka musu da alherinSa, mutane irinsu: Malam Ibrahim Akilu da Malam Tahir Yola da Malam Awwal Kunya da Malam Tijjani Damagaram da Malam Mujtaba Adam da dai sauransu.

Daga karshe, ina rokon duk wanda ya bude wannan shafi don dubawa, da yayi salatin Annabi ga iyayena da Allah Yayi musu rasuwa da niyyar ladan yaje gare su.

TUNASARWA

Duk wani wanda yake da wata tambaya (dangane da abin da muka rubuta), ko kuma neman karin bayani, ko kuma shawara da dai sauransu, yana iya rubuto min ta adreshi na na email da ke shafin farko.

Mai karatu, a sha karatu lafiya.