Daren (Lailatul) Kadri



Hakika Mu Muka saukar da shi (Alkur'ani) a cikin dare mai alkadari (lailatul kadri)* To me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul Kadri* Lailatul Kadri ya fi watanni dubu* Mala'iku da Ruhu (Mala'ika Jibril) suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu saboda kowane umurni* Sallama ne shi daren, har fitar alfijir*.

- Alkur'ani (97:1-5)


A wannan dare ta "Lailatul Kadri" ne Allah Madaukakin Sarki Ya sauka da dukkan Alkur'ani mai girma gaba dayansa daga "Lauhil Mahfuz" zuwa ga Manzon Allah (s). Allah Madaukakin Sarki Yana fadi cikin Alkur'ani cewa: "Hakika Mu Muka saukar da shi a cikin dare mai albarka…"(1) wannan dare kuwa shi ne Daren "Lailatul Kadri". To sai dai kuma daga baya Mala'ika Jibril (a.s) ya kan kawo wa Manzon Allah (s) ayoyin Alkur'anin a hankali a hankali har cikin shekaru 23.

To amma kuma yana da kyau a fahimci cewa ba wai farkon saukan ayoyin Alkur'ani a daren lailatul kadri ba ne, ko kuma wai an saukar da wasu ayoyin Alkur'anin a daren lailatul Kadri ba ne, don kuwa idan har haka ne, to wace falala wannan dare ya ke da shi kenan a kan sauran darare, tun da dai ai an saukar da wasu ayoyin ma a wasu dararen? Haka nan kuma ba wai an saukar da surar "Inna Anzalnahu" ba ce a wannan dare, saboda fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: "Hakika Mu Mun saukar da shi", don lamirin "shi" din yana komawa ne ga Alkur'ani ba wai ga ita kanta surar ko kuma wata aya ta cikinta ba ne.

Don haka saukar da Alkur'ani gaba dayansa ne aka yi shi a wannan dare mai albarka - daga "Lauhul Mahfuz" zuwa ga zuciyar Manzon Allah (s), kana daga baya kuma aka dinga sauko da ayoyin kadan-kadan, gwargwadon abin da ya faru a lokacin.

  • Ma'anonin Lailatul Kadri:
  1. An sanya wa wannan daren suna "Lailatul Kadri" ne don shi ne daren da Allah Madaukakin Sarki Ya ke kaddara abubuwa, Yake kaddara abubuwan da za su faru cikin shekara, na daga: rayuwa da mutuwa, alheri da sharri, arziki, haihuwa da dai sauransu. Muna iya tabbatar da hakan kuwa ta fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: "A cikinsa ne ake rarraba duk wani al'amari mai hikima* Al'amari ne daga wurinmu, hakika Mu Mun (kasance) Masu aikowa ne* Wata rahama ce daga Ubangijinka, hakika Shi Shi ne Mai ji Masani(2)".
  2. Don haka "raba al'amari mai hikima" yana nufin kaddara al'amurra da dukkan abubuwan da suka kumsa da kuma tabbatar da su a wannan dare mai albarka daga Allah Madaukakin Sarki zuwa ga bayinSa.
  3. Sannan kuma akan ce al-Kadr: da ma'anar matsayi, a kan ce masa (wato daren) "lailatul kadr" saboda muhimmanci da kuma matsayinsa, da kuma girman masu ibada a cikinsa. Don raya wannan dare da ibada da ayyuka na kwarai irin su salla, zakka da dai sauran ayyukan alheri, sun fi ayyukan da mutum zai yi cikin watanni dubu da babu "lailatul kadri" a cikinsu.
  • Ayyana Daren Lailatul Kadri:
Lalle Alkur'ani mai girma bai ayyana wani dare ne na Lailatul Kadrin ba, in dai ban da cewa dai ana samun daren ne a watan Ramalana mai albarka. Abin da kawai ya yi bayani da kuma ayyana wannan dare shi ne hadisi da ruwayoyi:
  1. An ruwaito daga Hassan bn Abu Ali yana cewa: Na tambayi Imam Abu Abdullah (a.s) kan "lailatul kadri", sai ya ce: "Ku nema shi cikin daren 19, 21 da 23(3)".
  2. Kusan dukkan ruwayoyin Ahlulbait (a.s) sun tafi a kan cewa ana samun wannan dare dai a kowace shekara, kuma a kan same shi cikin watan Ramalana, kuma yana cikin daya daga cikin wadannan darare guda uku ne muka ambata a sama. A saboda haka ne ma shi'a suke kiran wadannan darare uku a matsayin "Dararen Lailatul Kadri".
  3. Daga Zurara ya ce: 'Na tambayi Imam Bakir (a.s) kan lailatul kadri, sai yace min: "Yana cikin darare biyu, daren 21 da 23". Sai na ce masa, ka gaya min wanne ne a cikinsu, sai ya ce: "Kai dai ka yi aiki a cikinsu biyun, daya daga cikinsu dai shi ne "lailatul kadri(4)".
To abin da dai za mu iya fahimta shi ne cewa daren dai yana cikin daya daga cikin wadannan darare ne.

Haka nan kuma ba a ayyana lokacin da ake samun wannan dare ba a cikin dararen, don a ba wa mutum daman ci gaba da ibada dukkan daren, don kara samun lada da kuma neman gafarar Ubangiji.

  • Falalar Suratul Kadri:
  1. An samo daga Abu Abdullah (a.s) yana cewa: "Duk wanda ya karanta surar "Inna An zal nahu" cikin sallarsa ta farilla, wani mai kira zai ce "Ya bawan Allah, an gafarta maka zunuban da ka yi……(5)".
  2. An ruwaito Imam Bakir (a.s) yana cewa: "Duk wanda ya karanta surar 'Inna An zal Nahu', kuma ya bayyana muryarsa, kamar wanda ya fitar da takobinsa ne fi sabilillah (jihadi), wanda kuma ya karanta ta a boye da yawa, Allah Zai share masa zunubai dubu daga cikin zunubansa(6)".
  • Falalar Lailatul Kadri:
An so a yi wanka a wannan dare, ibada, addu'a, Ziyarar Imam Husain (a.s) da dai sauransu har zuwa fitowar alfijir. To daga cikin falalolin wannan dare kuwa, har da:
  1. Duk wanda ya tsaya (ibadu) a daren lailatul kadri, yana mai imani da neman lada, Allah Zai gafarta masa zunubansa da ya aikata.
  2. Lallai shaidan ya kan buya cikin wannan dare, ba zai fito ba har sai bayan fitowar alfijir din wannan dare.
  3. Albarkoki da ni'imomin Allah su kan sauka a wannan dare, haka nan kuma Ya kan kare mutum daga dukkan sharrorin da wani ya nufe shi da su.
  4. Da dai sauransu. Ana iya komawa ga littattafan da suka yi bayani a kan wannan dare.






____________
(1)- Surar Dukhan; 44:3.
(2)- Surar Dukhan; 44:4-6.
(3)- Al-Mizan fi Tafsiril Kur'an: 20/333.
(4)- Majma'ul Bayan: 9-10/787.
(5)- Majma'ul Bayan: 9-10/784.
(6)- Tafsirul Safi; 5:353.