JAGORAN MAI SALLA



Wannan shafi na tsara shi ne don yin bayanin yadda ake yin alwala da salla a mazhabar Ja'afariyya (Tafarkin Iyalan gidan Manzon Allah). Hakan kuwa ba don komai ba sai don saboda irin muhimmancin da salla ta ke da shi ne a rayuwar mu ta yau da kullum, wato matsayinta na ginshikin wannan addini namu na Musulunci, wacce idan tayi kyau dukkan ayyuka ma sun yi kyau idan kuwa ta baci to sauran ayyuka ma sun baci, Allah Shi kiyashe mu.
To don saboda irin wannan matsayi da salla take da shi ne na ga ya dace in bude wannan shafi, don mu koyi yarda ake salla da alwala a wannan tafarki na tsira. Da fatan Allah Zai sa mu cikin masallata.
Don haka sai mai karatu, ya zabi daya daga cikin wadannan maudhu'ai da suke kasa don ganin abin da ke cikinsa:

Alwala A Tafarkin Ahlulbaiti (a.s.)
Salla A Tafarkin Ahlulbaiti (a.s.)
Maganganu Kan Salla