Abul Fadhl al-Abbas Dan Imam Ali (a.s) - Gwarzon Karbala:
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Bisa abin da ya fi shahara, an haifi Sayyiduna Abul Fadhl al-Abbas ne a garin Madina a ranar 4 ga watan Sha'aban shekara ta 26 bayan hijirar Ma'aikin Allah (s). Mahaifinsa dai shi ne Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s), mahaifiyarsa kuwa ita ce Fatima bint Hazam bn Khalid bn Rabi' ibn Amir Kalbi wacce aka fi sani da Ummul Banin, wacce ta fito daga kabilar Kilah, daya daga cikin mafiya daukakan Bani Hashim da aka sansu da jaruntaka a fagen fama. Lokacin da labarin haihuwarsa ya kai ga mahaifinsa Imam Ali (a.s), Imam (a.s) ya yi sujada don nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki. Bayan kwanaki bakwai da haihuwar, kamar yadda sunna ta tanadar Imam Ali ya sanya wa wannan jariri suna Abbas.

Tarihi ya tabbatar da cewa bayan shahadar Fatima al-Zahra (a.s) da wasu shekaru, Imam Ali (a.s) ya bukaci dan'uwansa Akil da ya zaba masa wata mace wacce ta fito daga gidan ma'abuta jaruntaka don ya aura, don haka Akil ya zaba masa Fatima bint Hazam (Ummul Banin) don ya aure ta, haka kuwa lamarin ya kasance inda ya aure ta, Allah kuma Ya arzurta su da 'ya'ya hudu maza, wato Abbas, Abdullah, Ja'afar da Usman, wadanda dukkansu sun yi shahada a Karbala wajen taimakon Musulunci da kuma dan'uwansu Imam Husain (a.s). An ce dalilin da ya sa Imam Ali (a.s) ya bukaci a sama masa macen da ta fito daga gidan ma'abuta jaruntaka shi ne don ta haifa masa da namiji wanda zai taimaki dansa Husain (a.s) a nan gaba yayin da zai kasance shi kadai cikin makiya a Karbala. Ummul Banin dai ta kasance mai nuna tsananin kauna ga 'ya'yan Fatima Hasan da Husain (a.s) ta yadda tun farko-farkon shigowarta gidan Ali (a.s) ta bayyana musu cewar ita baiwarsu ce don haka tana fatan za su karbi wannan bukata tata, hakan kuwa ta ci gaba hatta bayan haihuwar 'ya'yanta. Har ila yau ta kasance mai mika wuya da bin Iyalan Gidan Manzon Allah (s) sau da kafa, musamman Imam Husain (a.s) wanda ta kasance tana sonsa fiye da 'ya'yanta, ta yadda hatta lokacin da labarin shahadar 'ya'yanta a Karbala ya isa gare ta, ba ta damu ba, abin da ke fita a bakinta kawai shi ne 'ina dana Husain ya ke'.

Abul Fadhl al-Abbas ya kasance kyakkyawan mutum, don haka ne ma ake kiransa da sunan Qamar Bani Hashim (Watan Bani Hashim) saboda kyaun da Allah Ya yi masa, ga shi kuma jarumi, mai juriya, mai hakuri da kuma imani da Allah.

Kamar yadda aka saba, Abbas ya tashi ne karkashin kulawar mahaifinsa Ali (a.s) har na tsawon shekaru 14, wato har zuwa lokacin da mahaifin nasa ya yi shahada. Daya daga cikin burin Imam Ali (a.s) shi ne wannan da nasa (Abbas) zai tashi ya kasance wa dan'uwansa Imam Husain (a.s) kamar yadda shi ya kasance ga Manzon Allah (s), wato dan'uwana kuma mabiya mai bi sau da kafa kana kuma garkuwa mai kare Ma'aiki daga dukkan wani sharri, saboda masaniyyar da yake da ita, kamar yadda Manzon Allah (s) ya sanar da shi, na abin da zai samu dansa Husain a Karbala. Daga nan kuma sai kulawarsa ta koma hannun dan'uwansa Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) har na tsawon shekaru goma, sauran shekaru goma na rayuwarsa kuma karkashin dan'uwansa kuma shugabansa Husain (a.s). Ba abin mamaki ba ne idan aka ga Abul Fadhl al-Abbas da halaye na kwarai na madalla, da suka hada da kwarjini, ban tsoro (ga makiya), karfin gwuiwa, jaruntaka da fuskantar makiya babu tsoro ba ja da baya da ya gada daga wajen mahaifinsa Ali (a.s), hakuri da juriya da ya gada a wajen dan'uwansa Hasan (a.s), da kuma ruhin sadaukarwa da tsayin daka da da'a ga shugaba da ya samo daga wajen dan'uwansa Husain (a.s). Don haka ana iya cewa a kowani bangare, Abbas (a.s) a shirye yake don fuskantar kalubalen da ke gabansa na taimaka wa Musulunci a lokacin da makiya suka yunkuro wajen hadiye shi, kamar yadda mahaifinsa ya yi a lokacin Manzon Allah (s), ba ya ga dimbin ilmin da yake da shi da kuma ruhin taimakawa marasa shi da yin biyayya ga dokokin Allah.

A hakikanin gaskiya ana iya cewa matsayin Abbas a wajen Imam Husain tamkar matsayin Ali ne a wajen Manzon Allah (s), sanin hakan ne ya sanya tun farko Ali (a.s) ya yi kokarin kulla alaka ta kut da kut tsakanin wadannan 'yan'uwa biyu da samar da yanayi ta shakuwa tsakaninsu. Daya daga cikin abin da ke dada tabbatar da hakan shi ne abin da aka ruwaito daga gare shi yayin da yake kwance a gadon shahadarsa bayan sarar da la'anannen Allah Ibn Muljam ya yi masa a masallaci. An ce a wancan lokacin Ali (a.s) ya yi umarnin da a kira masa dukkanin iyalansa. Bayan isowarsu gaba daya sai ya mika kulawarsu ga hannun babban dansa Imam Hasan (a.s) in banda Abul Fadhl al-Abbas, wanda a lokacin bai wuce dan shekara 12 a duniya ba. Ganin haka sai Abbas ya koma gefe yana kuka, sai Ali (a.s) ya kira shi kusa da shi ya kama hannunsa da mika shi ga Imam Husain (a.s) yana mai cewa: "Ya Husain, na mika kulawar wannan yaro gare ka. Zai wakilce ni a ranar da za ka yi gagarumar sadaukarwa, zai ba da rayuwarsa wajen kare ka da sauran na kurkusa da kai". Daga nan sai ya juya wajen Abbas ya ce masa: "Ya kai dana Abbas, na riga da na san irin kaunar da kake yi wa Husain, duk da cewa a halin yanzu shekarunka sun yi karinci wajen gaya maka abin da zai faru, amma dai idan wannan rana ta zo, ka da ka dauki duk wata sadaukarwar da za ka yi wajen kare Husain da 'ya'yansa a matsayin sadaukarwa mai girma da ba ta cancance su ba". Sanin hakan ne ma ya sanya mahaifiyar Abbas, Ummul Banin, jin kadan kafin Husain (a.s) ya bar Madina a hanyarsa ta zuwa Karbala ta kira 'ya'yanta da bayyana musu cewar: "Ya ku 'ya'yana, ku sani cewa, a daidai lokacin da na ke matukar sonku, Imam Husain shugabanku ne. Don haka idan kuka bari wani abu ya same shi ko 'yan'uwansa mata ko kuma 'ya'yansa alhali kuna raye to ban yafe muku ba".

A gaskiya ba za a iya siffanta irin biyayya da kaunar da Abbas ke nuna Imam Husain (a.s). An bayyana cewa wata rana Imam Husain ya ji kishirwa a lokacin suna tare da mahaifinsa a masallacin Kufa, don haka ya bukaci Qambar, daya daga cikin masu hidima wa Imam Ali (a.s), da ya taimaka masa da ruwa. Jin haka sai Abbas ya mike da gudu don ya kawo wa Husain (a.s) ruwa, saboda gaggawar da yake yi wajen kawo ruwan duk ya jika jikinsa. Ganin haka sai Imam Ali (a.s) wanda a lokacin yana cikin huduba ne a masallacin ya yanke hudubar, hawaye na zubo masa. Lokacin da aka tambaye shi dalilin kukansa sai ya bayyana cewar: "Saboda wannan Abbas din da a yau ya jika jikinsa da ruwa a kokarin da yake yi na kashe kishirwan dan'uwansa Husain, wata rana zai jika jikinsa da jininsa a kokarin kashe kishirwar 'ya'yan Husain".

Jaruntakar Abul Fadhl al-Abbas (a.s):

Rayuwar Abbas (a.s) cike take da biyayya da kuma ruhin kare Musulunci sakamakon irin jaruntakar da yake da ita. To ai hakan ba abin mamaki ba ne idan aka yi la'akari da waye mahaifinsa wanda ake kiransa da sunan 'Zakin Allah' saboda irin jaruntakarsa. Don haka Abbas ma haka ya taso cikin irin da irin wannan jaruntaka. Bari mu ga kadan daga cikin jaruntakarsa a fagen fama.

Yakin farko da Abbas ya fara halarta shi ne Yakin Siffin da ya gudana tsakanin rundunar gaskiya karkashin jagorancin mahaifinsa da kuma ta karya da wuce gona da iri karkashin jagorancin Mu'awiyya bn Abi Sufyan alhali a lokacin yana dan shekaru 11 ne a duniya. An bayyana cewar wata rana Abbas ya rufe fuskarsa ya fito filin daga ba tare da an gane ko wane ne ba. Ganin haka sai daya daga cikin jaruman sojojin Mu'awiyya da ake kira da Ibn Shasa ya umarci daya daga cikin 'ya'yansa bakwai da sare wuyansa (saboda ganin yaro ne), nan take Abbas ya aika da shi lahira. Ganin haka sai ya sake turo wani dan nasa, haka dai Abbas ya dinga gamawa da su har ya'yansa bakwai suka kare amma ba tare da sun sami nasarar kashe Abbas ba. Ganin haka sai shi da kansa ya fito, Abbas ya yi nasara a kansa, wannan ya sanya kowa da ke wajen mamaki, don haka suka tsorata babu wani da ya iya sake kusato shi. Sai bayan da ya cire abin da ya rufe fuskansa ne mutane suka fahimci ko shi wane ne.

Wani abu kuma da ke nuni da jaruntakar Abul Fadhl al-Abbas (a.s), a bangare guda kuma da irin kauna da mika wuyarsa ga Imam Husaini (a.s), shi ne batun afuwa da kariyar da Shimr bn Zil Jawshan, daya daga cikin manyan kwamandojin Yazid a Karbala (wanda kuma yake matsayin kawu ga Abbas), ya nemi ya bai wa Abbas da sauran 'yan'uwansa. Lamarin dai ya faru ne lokacin da Shimr din ya taho sansanin Imam Husain (a.s) ya ce: "Ina 'ya'yan 'yar'uwata, wato Abbas, Abdullah, Ja'afar da Usman? Amma (Abbas) yayi shiru bai ce masa komai ba har sai lokacin da Imam Husaini (a.s) ya ce masa: "Ka amsa masa mana ko da dai fasiki ne, amma ai yana daga cikin kawunanku". Sai Abbas ya ce masa: "Me kake so"? Sai ya ce: " Ya ku 'ya'yan yar'uwata kuna cikin aminci, na bukaci kariya gare ku daga Ibn Ziyad, amma me ya sa kuke son kashe kanku tare da Husain? Me zai hana ba za ku shigo cikin dakarun Yazid ba? Nan take sai Abbas ya amsa masa da cewa: Allah Ya la'ance ka, Ya kuma la'anci kariyarka (amincinka), shin za ka ba mu kariya ne alhali dan Manzon Allah ba shi da kariya?!

Har ila yau wani lamari makamancin hakan ya faru, wato lokacin da wani dan'uwar mahaifiyar su Abbas din mai suna Jarir bn Abdullah, wanda shi ma ya bukaci Ibn Ziyad da ya yi afuwa wa 'ya'yan 'yar'uwar tasa wato Abbas da 'yan'uwansa, don haka bayan da Ibn Ziyad ya amince masa sai ya rubuta wasika ga Abbas yana kiransa da su bar rundunar Husain (a.s) su dawo ta Yazid don su ceci rayukansu (kamar yadda ya ce). A nan ma dai Abbas ya bula masa kasa a ido lokacin da ya yaga wannan wasikar ya ce a je a gaya masa cewa: Ba za mu taba barin Husain mu nemi kariyar Ibn Ziyad ba. Muna neman taimako da yardar Allah, don haka a shirye muke mu sadaukar da rayukanmu ga abin kaunarmu Husain da kuma Musulunci".

Ko ba a fadi ba wadannan matsaya guda biyu da Abbas ya dauka suna nuni da jaruntakarsa da kuma kaunarsa ga Imam Husain (a.s), saboda a lokacin ya tabbatar da cewar suna fuskantar mutuwa ne, babu makawa cikin haka, amma yana da zabin ya yi watsi da Husain (wal iyazu billah) ya koma rundunar makiya don ya tseratar da rayuwarsa, kamar yadda ma shi kansa Imam Husain din ya bukaci mabiyansa da su yi, inda yake ce musu: suna iya amfani da duhun dare su gudu don makiya shi suke nema ba su ba, amma Abbas (da sauran sahabban Husaini) ba su yi haka ba, saboda jaruntaka da kuma mika wuya ga Husain (a.s).

Jaruntakar Abul Fadhl al-Abbas (a.s) A Karbala:

Lokacin da kishir ruwa ta yawaita a sansanin Imam Husain (a.s) sakamakon hana isar ruwa wajen da sojojin Yazid suka yi, Imam Husain (a.s) ya bukaci dan'uwansa Abbas da ya samo ruwa a kogin Furat don a samu na sarrafawa, ba tare da bata lokaci ba ya dauki jakar ruwa ya nufi wajen da ruwan yake, sai dai sojojin Yazid sun yi kokarin hana shi isa, amma ina yace da wa aka hada ni ba da ku ba, inda ya yi musu kaca-kaca ya isa ga kogin Furat din ya debo ruwan, amma duk da haka sai Umar bn Sa'ad ya sake turo wata runduna ta sojoji da su hana shi isar da ruwan sansanin Husain (a.s). Nan ma dai aka ta gumurzu tsakanin sojojin makiya da Abbas a kokarin da yake yi na isar da ruwan sansanin Husain. A wannan karon ma Abbas ya nuna wa duniya cewa shi jinin Amirul Muminina Ali (a.s) ne inda ya tunkarin sojojin makiya da sara da bugu, ya kashe na kashewa ya raunana na raunanawa. Rundunar makiya ta watse, kowa na shakkun matsowa kusa da shi, ganin haka sai wani daga cikin sojojin makiya mai suna Zaid bn Waraqa' da taimakon Hakim bn Tufail ya lababo ta bayan bishiyar dabinon da ke wajen ya sare hannunsa na dama, Abbas ya mai da takobi hannun hagu ya ci gaba da yaki, nan ma dai wani kafirin Hakam bn Tufail al-Ta'i ya lababo ya sare hannunsa na hagun, duk da haka Abbas ya ci gaba da yaki ya ci gaba da kare wannan jaka ta ruwa da bakinsa don kada ta fadi ta zube, ko zai iya samun damar isar da ita sansanin Husain (a.s) don yara da mata su sami abin jika makogoronsu.

Duk dai da irin wannan hali da yake ciki makiya na tsoro kusato inda ya ke, don haka sai suka harbo wasu kibiyoyi guda biyu, daya ta sami idonsa, dayar kuwa ta huda wannan jaka ta ruwa, ruwa ya tsiyaye. Ganin haka sai jikinsa ya yi sanyi, ya san cewa ba zai sami damar cika burinsa na kai wa yara da mata ruwa ba. Ganin irin wannan hali da yake ciki, makiya kuwa wadanda da man duk sun gudu sai suka dawo suka kewaye shi, wani ya matso ya kwada masa wani kulli na karfe a ka, nan take ya fadi kasa cikin turbayar da ke wajen da ke cike da kuna saboda zafin rana. A nan dai ya tabbatar da rayuwarsa ta kare, to amma babban burinsa shi ne ya ga dan'uwansa Husain kafin cikawarsa, don haka sai ya daga murya ya ce: "Ya Shugabana, ka iso gare ni kafin in cika".

Jin wannan kira sai Imam Husain (a.s) ya garzayo ya keto cikin makiya tamkar namijin zaki, ya iso wajensa, ya tsaya a kan dan'uwansa, ya durkusa ya dauki kansa ya dora a kan cinyansa yana mai cewa: "Ya dan'uwana Abbas, me suka maka ne?", Husain (a.s) ya fashe da kuka saboda ganin irin halin da dan'uwan nasa ke ciki.

Burin Abbas na sake ganin dan'uwansa dai ya cika, don haka sai ya ce masa:

"Ya Shugabana, ina da wasu bukatu na karshe da nake son in bayyana maka. Lokacin da aka haife ni fuskarka na fara gani, don haka bukatata ta karshe ita ce in ga fuskarka yayin mutuwa ta. Kibiya ta fasa min idona guda, dayan kuma yana cike da jini, ko za ka share min daya ido ko zan samu damar ganinka in cika burina na karshe. Bukatata ta biyu ita ce idan na mutu, kada ka dau gawata zuwa sansaninka, don kuwa na yi alkawarin kawo wa Sakina ruwa, don haka tun da na gaza wajen kawo mata ruwan, ba zan iya fuskantarta ko da bayan mutuwa ne, duk da cewa na san wahalhalun da ka shiga ciki tun daga safiya zuwa yanzu sun cutar da kai, daukar jikina zuwa sansaninka ma wani babban aiki ne. Bukatata ta uku ita ce kada a kawo Sakina wajen nan ta ga halin da nake ciki, na san irin kauna da soyayyar da take da shi gare ni, ganina haka kwance a irin wannan hali zai iya sanadiyyar mutuwarta".

Cikin hawaye Husain (a.s) ya yi masa alkawarin cika wannan bukatu nasa, sai dai shi ma ya shaida wa Abbas cewa yana da wata bukata da yake so ya cika masa, ita ce kuwa:

"Ya Abbas, tun yarintarka ka ke kirana da sunan shugaba, ko da sau daya ne ka kira ni da sunan 'dan'uwa'".

Daga nan sai Husain (a.s) ya share masa jinin da ke idonsa, ya dube shi ya ce: Ya dan'uwana! Ya dan'uwana!. Da wadannan kalmomi ne ya ja numfashinsa na karshe. Husain ya fadi a jikinsa yana kuka, yana cewa: "Yanzu kan an karya min kashin baya".

Wannan ma yana nuni da irin jaruntakar Abbas da kuma mika wuyarsa ga shugabansa Imam Husain (a.s).

Abbas dai ya yi shahada ne yana dan shekara 35 a duniyar a ranar 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki (s).

Abbas (a.s) ya yi shahada yana da mata guda, Lubaba 'yar Ubaidullah bn Abbas bn Abdul Mutallib, yana da 'ya'ya biyu Muhammad da Fadhl.

Amincin Allah Ya tabbata a gare ka, Ya Abbas, ranar da aka haife ka, da ranar da ka yi shahada da ranar da za a tashe ka karkashin tutar kakanka Manzon Allah (s).