ADDU'AR SUHUR
Bismillah

Cin abinci ko abin sha don yin Suhur yana da matukar muhimmanci da kuma lada mai yawa ga mai azumi. Akwai ruwayoyi daban-daban da suke kira da yin suhur koda da ruwa ne kawai saboda muhimmancinsa. Ga kadan daga cikin irin wadannan ruwayoyi da suke magana kan Suhur:

Manzon Allah (S) yana cewa: "Allah da ManzonSa suna salati ga masu neman gafara da masu yin suhur a lokacinsa. don haka ku yi Suhur koda da ruwa ne"

Manzon Allah ya ce: "Suhur albarka ne, don haka kada ku bar suhur koda kuwa da gutsuren dabino ne".

Haka nan kuma Imam Sadiq (a.s) ya ce Manzon Allah (s) ya ce: Ku yi Suhur koda da (kofin) ruwa ne, Lalle amincin Allah ya tabbata ga masu yin Suhur


Haka nan kuma a lokacin Suhur din an so a karanta wasu addu'o'i da aka ruwaito daga Manzo da Alayensa (a.s). Daga cikin wadannan addu'o'i akwai wannan addu'a ta kasa:

supplication

Niyyar Daukan Azumi.

Niyya dai ba wata aba ba ce face dai kawai mutum ya kudura cikin zuciyarsa cewa zai yi azumi don neman kusanci da Allah Madaukakin Sarki, ba lalle ne sai ya furta da fatan bakinsa ba