Nasarorin Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran:
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Marigayi Imam - Dukkan Tunaninsa Shi Ne Yadda Musulunci da Musulmi Za Su Ci Gaba

Hakika nasarar da Juyin Juya Halin Musulunci na Iran karkashin jagorancin marigayi Ayatullah Imam Khumaini (r.a) ya samu a ranar 11 ga watan Fabrairun 1979 ya haifar da abubuwa da yawa da kuma tabbatar da wasu masu dama wadanda kafin hakan an rasa su ko kuma ma ana tunanin ba za su iya samuwa ba sakamakon jahilcin masu wannan tunani ko kuma kin gaskiyarsu saboda wasu manufofi na ta daban. Ko ba a fadi ba daga cikin irin nasarori da abubuwan da juyin ya tabbatar sun hada har da: tabbatar da rashin ingancin raba addini da siyasa, tabbatar da karfin addinin Musulunci da Shi'anci wajen iya gudanar da harkokin al'umma, tabbatar da karfi da rinjayen imani da hadin kan al'umma a kan duk wani karfi na duniya, tabbatar da karfin malaman addini wajen jagorancin wani yunkuri na siyasa da kuma jagorancin al'umma, yada kishin addini da riko da shi a duniyar musulmi, riko da koyarwar Musulunci irinsu sanya hijabi da dai sauransu, haifar da hadin kai tsakanin musulmi (shi'a da sunna), kaskantar da kasashen duniya ma'abuta girman kai, daukakar musulmi da dawo musu da mutumcinsu da dai sauran abubuwa masu daman gaske da suke a fili kamar hasken rana. Wadannan abubuwa su ne abin da nake son karin bayani kansu a dan wannan rubutu, duk da cewar, saboda takaitawa, ba zai yiyu in kawo su gaba daya ba, face dai zan yi magana ne kawai kan ukun farko, watakila idan har muna raye, sauran a yi magana a kansu a nan gaba.

1- Tabbatar Da Rashin Ingancin Raba Addini Da Siyasa:

A karnin baya-bayan nan duniya ta shaida kokarin mai yawan gaske da aka dinga yi wajen yada farfagandan raba addini da siyasa - shin a bangaren tunani da akida ne ko kuma a bangaren ilmi da gudanarwa ne -. Idan muka yi dubi za mu ga cewa wasu kungiyoyi biyu ne suka ba wa kansu aikin yada wannan farfaganda: kungiya ta farko ita ce wacce ta ginu a kan jahilci da takaita tunaninta ta biyu kuwa ita ce wacce take yin hakan bisa ilmi don cimma wata manufa da take son cimmawa kamar yadda za mu gani nan gaba. Kungiyar farko dai ta kasu kashi biyu:

Kashin farko su ne irin mutanen nan da aka bar su a baya duk kuwa da cewa wasunsu ma masana ne na addinin Musulunci to amma saboda takaita tunaninsu da suka yi kan nassosin musulunci da kuma ganin yadda siyasa ta baci sakamakon ayyukan wasu baragurbi ya sanya su kira zuwa ga raba addini da siyasa, sai dai kuma sun rufe idanuwansu kan wasu asasi na addini da hakika ta rayuwa. Dangane da wadannan mutane, marigayi Imam Khumaini, cikin wasiyyarsa ta karshe yana cewa: "Dole ne a gaya wa wadannan jahilai cewa Alku'rani mai girma da hadisan Ma'aki (s.a.w.a) cike suke da hukumce-hukumce hukuma da siyasa sama da yadda suke da shi kan sauran abubuwa, kai mafi yawa daga cikin hukumce-hukumcen ibada da suke cikin Musulunci na siyasa ne…Manzon Allah (s.a.w.a) ya kafa hukuma kamar sauran hukumomi na duniya sai dai shi da manufa ce ta yada adalci, hukumar gaskiya ta taimakon marasa galihu da kuma jan burki ga ma'abuta zalunci. Hakika tsayar da adalci na daga cikin mafi girman wajibai kana kuma daga cikin mafiya girman ibada".

A wurare da dama dai Imam ya kasance yana ishara da wannan lamari, inda a wani sashi na wasiyyar tasa ma yake cewa: "Mas'alolin Musulunci mas'aloli ne na siyasa kuma sun fi rinjaye kan sauran abubuwansa" a wani wajen yana cewa: "Irin ayoyi da hadisan da suka zo kan siyasa ba su zo kan ibada ba, ku duba ku ga litattafan fikihu ku gani za ku ga cewa wasu sassa kadan ne daga cikinsu suke magana kan ibada sauran duk kan batun siyasa, zamantakewa da dai sauransu suke magana…don haka Musulunci addini ne na siyasa da hukama".

Kashi na biyu na kungiya ta farko kuwa su ne irin mutanen nan da su ba musulmi ba ne duk da cewa suna ikirarin bin sauran saukakkun addinai, to amma ba su da cikakken imani da masaniyya ta sosai kan addinin da suke bi. Mafiya yawa daga cikin irin wadannan mutane masu akidar nan ne ta humanism da suke ganin dan'Adam shi ne zai iya tsara wa kansa rayuwa ba wani ba, don haka ne dangane da mas'alolin siyasa da gudanar da hukuma ba sa ganin addini yana da wani rawar da zai iya takawa. Da dama daga cikin masu wannan ra'ayi sun samo shi ne sakamakon irin gazawar da malaman coci-coci da fada-fada suka yi a bangaren siyasa da kuma irin danyen aikin da suka dinga tabkawa a shekarun baya a kasashen Turai da sauran wurare, hakan ne ya haifar musu da wannan tunani na raba addini da siyasa. Wasu kuma daga cikin 'yan wannan kungiya tun asali ma ba su yarda da Allah ba, hakan ne ya sanya suke ganin wajibcin raba da addini da siyasa.

Su kuwa 'yan kungiya ta biyu da ke ganin wajibcin raba addini da siyasa su ne mutanen da suke yada wannan akida cikin sani kuma da gangan saboda cimma manufar fada da tasirin da addini yake da shi wajen tsara rayuwar al'umma da gudanar da hukuma. A takaice dai wadannan mutane da gangan suke yada wannan akida. Mafiya yawa daga cikinsu masu tsananin adawa ne da addinin musulunci, 'yan amshin shatan manyan kasashen duniya ma'abuta girman kai ne da kuma hukumomin kama karya masu shan jinin al'umma duk tsawon tarihi. Dalilinsu na yin hakan kuwa shi ne kokarin dushe matsayin addinin musulunci na fada da zalunci da babakere, don kuwa suna da cikakken masaniyya kan koyarwar musulunci a wannan bangare. Don haka ne za ka ga sun fi gudanar da ayyukansu da kuma yada wannan farfaganda a kasashen da musulmi suka fi yawa don kada su bari addinin musulunci ya shigo cikin siyasa da wayar da kan al'umma, don ta hakan suna iya rasa matsayin da suke da shi da suke amfani da shi wajen zaluntar al'umma. Kasar Iran dai tana daga cikin irin wadannan kasashe da shekara da shekaru 'yan mulkin mallaka suka yi suna ta kokari wajen ganin hukumce-hukumcen Allah ba su samu gindin zama ba. Dangane da 'yan wannan kungiya, Imam Khumaini, mu'assasin juyin juya halin Musulunci, yana cewa:

"'Yan mulkin mallaka ne suke cewa dole ne a raba addini da siyasa kuma wai bai kamata malamai su tsoma baki cikin harkokin siyasa ba, wannan batu ne da marasa addini suke yadawa."

Har ila yau a cikin wasiyyarsa Imam yana cewa: "Daga cikin muhimman makirce-makircen da suka bayyana ake ganinsu a fili cikin wannan karnin, musamman ma a wannan zamanin bayan nasarar Juyin Musulunci, akwai dogewa da aka yi kan farfaganda ta fuskoki daban-daban don sa al'ummomi musamman ma jarumar al'ummar Iran su yanke kauna daga Musulunci. Wani lokaci a fili kuma kai tsaye ake nuna cewa hukumce-hukumcen Musulunci wadanda aka shimfida su tun shekaru dubu da dari hudu da suka wuce, ba za su iya tafiyar da al'amuran kasashen duniya a wannan zamani ba. Ko kuma wai Musulunci addini ne na koma-baya wanda bai yarda da kowace irin ci gaba da kuma abubuwa na zamani ba. Kuma wai babu yadda za a yi a wannan zamani kasashen duniya su juya baya wa ci gaba da wayewa, da dai irin wadannan farfadandoji na wauta. Wani lokaci kuma don tsananin makirci da shedanci sukan fito ne ta fuskar goyon bayan rayuwar sufanci a Musulunci. Wai addinin Musulunci kamar dai sauran addinai, bauta ce kawai tsantsa da tsarkake zuciya da guje wa mukamai na duniya da kuma kira zuwa ga yin watsi da ita duniyar saboda a samu a shagala da ibada da zikiri da addu'oi don neman kusanci ga Allah da nisantar duniya. Haka nan wai siyasa da hukuma da tafiyar da al'amuran kasa duk sun saba wa wannan babbar manufa da buri na addini…".

Ala kulli halin dai, abin tambaya a nan shi ne mene ne ya sa suka dauki wannan mataki? To daga cikin manyan dalilan da ya sa suka dauki wannan matsaya dai har da:

a) Tsoron musulunci da irin karfin da yake da shi: A fili 'yan mulkin mallaka sun san cewa addinin musulunci dai addini ne mai girma da karfi sannan kuma yana adawa da haramtattun manufofinsu, sun kuma san cewa a duk lokacin da ya samu tsayuwa da kafafunsa da kuma kafa hukuma to kashinsu ya bushe, wato ba za su samu damar isa ga wadannan manufofi nasu ba.

b) Raba malamai da al'umma da kuma hukuma: 'Yan mulkin mallaka sun fahimci cewa hada addini da siyasa na nufin kenan malamai za su sami bakin magana da kuma ba da gudummawa wajen gudanar da hukuma, wanda hakan abu ne da ba zai yi musu kyau ba saboda riko da addinin musulunci da aka san malamai da shi. Tarihi dai ya tabbatar da cewa a ko da yaushe malaman musulunci na hakika sun kasance ne tare da al'umma musamman wadanda ake zalunta da kuma marasa galihu daga cikinsu sannan kuma ba sa zama inuwa guda da azzalumai masu shan jinin al'umma, kamar yadda kuma a koda yaushe suke kokarin ganin an gudanar da dokoki da hukumce-hukumcen musulunci da suka ginu a kan adalci da daidaituwa tsakanin al'umma sabanin tsarin 'yan mulkin mallakan. Dangane da hakan da kuma batun makircin makiya na raba siyasa da addini an jiyo Imam yana cewa: "….wannan maganganun 'yan mulkin mallaka da 'yan koransu ne saboda addini ya kauce daga lamurran duniya da tsara rayuwar al'umman musulmi da kuma raba mutane da malamai a tafarki gwagwarmaya da 'yanto al'umma. Idan har suka sami nasarar haka za su mulki al'umma da sace musu dukiya. Wannan dai ita ce manufarsu"

c) Kyamar da addini yake wa duk wani nau'i na zalunci da lalata: Abu ne da yake a fili cewa 'yan mulkin mallaka da sauran ma'abuta son duniya ba za su taba amincewa ma'abuta addini da malamai su kasance a kan gaba wajen gudanar da mulkin al'umma ba, don kuwa sun san cewa hakan zai iya hana su isa ga bakar aniyarsu ta zaluntar al'umma da mai she su bayi.

d) Gamayyar harkokin Musulunci da kuma cewar sakon Musulunci bai san wata iyaka ta kasa da kasa ba, wato Musulunci ba addini ne na wata kasa ko al'umma guda ban da daya ba, addini ne na dukkan duniya, don haka 'yan mulkin mallaka sun riga da sun san cewa matukar Musulunci ya samu kafuwa da samun ikon gudanarwa a kasashe daban-daban na duniya, to lalle ba za su samu damar baza faratunsu na zalunci da shan jinin al'umma ba.

e) Kawo karshen hukumomin da ba su ginu a kan zabin al'umma da yardarsu ba. Da dama daga cikin shuwagabannin kasashe, musamman ma kasashen musulmi suna tsoron kafa hukuma karkashin jagorancin addinin Musulunci, don kuwa sun san cewa matukar Musulunci ya zo to babu makawa zai yi waje da hukumominsu da ba su dare mulki karkashin ra'ayin al'umma ba. Wannan dalili ne ya sanya a ko da yaushe suke goyon bayan 'yan mulkin mallaka da kuma duk wani kira na raba siyasa da addini.

A takaice dai, dukkan wadannan kungiyoyi biyu masu goyon bayan raba siyasa da addini, shin wadanda suke yi hakan bisa jahilci da rashin sani ko kuma wadanda suke yi cikin sani da ilmi, sun yi imani da abu guda shi ne kuwa wajibcin raba addini da siyasa ko da kuwa akwai banbanci tsakaninsu wajen niyya da manufa. To sai dai nasarar juyin juya halin Musulunci da aka samu a kasar Iran da kuma kafa hukuma ta addini ta kawo karshen wannan ra'ayi nasu da tabbatar da rashin gaskiyarsa. Don kuwa juyin a rubuce da aikace ya tabbatar da cewa ba wai kawai ma addini da siyasa ba za su taba rabuwa ba ne, face ma dai ya tabbatar da cewa siyasa da addini wasu abubuwa ne guda biyu da ba za su taba rabuwa da juna ba, ya tabbatar da cewa addinin Musulunci addini ne na zamantakewa da hukumci, ba wai addini ne da ya takaita kan 'yan wasu ibadu da dabi'u na daidaiku ba.

Hakika wannan juyi ya haskaka duniyar musulmi da haske mai haskakawa da kuma wayar da kan musulmi cewa addininsu ma fa yana da wata rawa da zai iya takawa a rayuwar yau da kullum sabanin yadda makiyansu suke tunani. Sanann kuma har ila yau, juyin ya kawo karshen makircin 'yan mulkin mallaka na yada ra'ayin raba siyasa da addini da kuma wayar da kan sauran musulmi da cikin jahilci suke yada wannan ra'ayi.

2- Tabbatar Da Karfin Musulunci Da Shi'anci Wajen Iya Gudanar Da Harkokin Al'umma:

Duk wani nau'i na gwagwarmaya, yunkuri ko kuma juyi yana bukatuwa da wani karfi da zai juya shi da isar da shi zuwa ga manufar da yake son cimmawa. Matukar ya rasa wannan karfi da goyon baya na tunani da imani to lalle babu inda zai je. A hakikanin gaskiya, isa ga manufa da samar da karfafaffen juyin juya hali yana bukatuwa da abubuwa masu motsarwa da kwadaitarwa.

Kowani mutum ko kuma jama'a akwai wasu abubuwa da suke zaba don zamantowa abubuwan da za su motsa su wajen haifar da juyin da suke son haifarwa. Misali, wasu abubuwan duniya ne, kamar samun kyakkyawar rayuwa ta duniya da suka hada da jin dadi, gida, abin sa wa a baki da dai sauransu, suke sanya su mikewa. Wasu kuma neman 'yanci da walwala ne ya ke sanya su mikewa, don haka sai su yi amfani da shu'urin mutane ma'abuta son 'yanci don cimma wannan manufa. Wasu kuma kishin kasa da 'yan kasanci ne suke amfani da shi wajen motsa zukatan masu wannan ra'ayi. Wasu kuma suna amfani ne da kabilanci da batun launin fata wajen motsa zukatan mutane wajen motsawa da haifar da juyi. Akwai dai abubuwa daban-daban da suke sanya haifar da wani yunkuri ko kuma juyi sai dai kawai za mu takaita ne da wadannan saboda kada mu tsawaita.

To amma akwai kuma wani abin na daban wanda kuma yake da muhimmanci kan wannan batu da muke yi na juyin juya halin Musulunci na Iran wanda kuma da shi ne za mu rufe batun da muke magana a kai. Wannan abu kuwa shi ne Musulunci wanda shi ne ya taka gagarumar rawa wajen haifar da juyin na Iran da kuma samun nasararsa. Tsawon tarihi dai, Musulunci ya nuna kansa a matsayin abin dogaron al'umma wajen kawo canji da samar da nasara a duk lokacin da wata al'umma take son fita daga cikin wani hali na kunci da take ciki, musamman ma idan har aka dogara da koyarwa irinta Ahlulbaiti (a.s) wato shi'a kenan. Tafarkin shi'anci, duk tsawon tarihin Musulunci, tun daga lokacin yunkurin Shugaban Shahidai Imam Husaini (a.s), har zuwa yanzu, cike yake da yunkuri na 'yantar da al'umma daga tafarkin shaidanun mutane masu kokarin kawar da al'umma daga bautar Allah zuwa ga bautan waninSa.

Mai yiyuwa ne tun farko a samu wasu mutane, sakamakon karancin hangen nesa ko kuma rashin masaniyya, hatta cikin malamai da makarantun addini, su yi zaton cewa abu ne mai wahala a wannan zamani juyin Musulunci ya iya yin nasara, hakan ne ma ya sa wasu suka nuna rashin amincewa da wannan yunkuri na Imam ko kuma alal akalla ba su ba shi kulawar da ya kamace shi ba. Irin wannan tunani hatta cikin wasu kungiyoyin masu gwagwarmaya ma akan same shi. To sai dai nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran ba wai kawai a rubuce ba hatta a aikace ya tabbatar da cewar Musulunci yana da karfin da zai iya jagorantar wani juyi sama da dukkan abubuwan da muka ambata a baya. Don haka ne Mu'assasin wannan juyi kana kuma jagoransa, Imam Khumaini, ya ke cewa:

"Wadanda suke tunanin cewa ba za a iya motsa mutane da Musulunci ba, ya kamata su fahimci cewa Musulunci shi ne mafi girman abin motsa mutane. Alkur'ani mai girma dai littafi ne na motsa mutane", "Karfin Musulunci ne ya sanya wata al'umma hannu rabbana ta yi galaba kan wasa azzalumar gwamnati ma'abuciya karfi",

Har ila yau Fidel Castro, shugaban kasar Kuba, a wata ganawa da ya yi kwanakin baya da ministan kiwon lafiya na Iran cewa yake: "Bayan faduwar tarayyar Sobiyeti na fahimci wasiyyar Ayatullah Khumaini ga Gorbacheb sannan kuma na yi imani cewa tsarin Alkur'ani da jagorancin jagoran Iran shi ne tsarin da ya kamata ya canji tsarin yammaci". Haka nan kuma a ruwaito babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Habib Chatty, a farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran yana cewa: "Wannan juyi na Musulunci daya ne daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a wannan karni, kuma ya tabbatar wa kowa cewar lalle Musulunci yana da karfin gaske. Hakika juyin Iran ya yi nasarar kawar da daya daga cikin gwamnatoci mafi girma". Shi ma a nasa bangaren Shahid Fathi Shikaki, tsohon shugaban kungiyar Jihadi Islami ta kasar Palastinu cewa ya ke: "Tasirin juyin Musulunci karkashin jagorancin marigayi Imam ya fi bayyana ne a kasar Palastinu, don kuwa al'ummar Palastinu, sakamakon mamayan haramtacciyar kasar Isra'ila, sun kasance cikin yanke kauna. To amma zuwan Imam ya ba su kyakkyawar fata da kuma tabbatar musu da cewa ta hanyar dogaro da Musulunci za su iya mikewa don 'yanto kansu". Da dai sauran irin wadannan maganganu da rahotanni da ba sa kirguwa da suke tabbatar wa al'umma irin karfin da Musulunci yake da shi wajen 'yanto su, wanda hakan kuwa an same shi sakamakon wannan juyi da Imam ya jagoranta.

3- Tabbatar Da Karfi Da Rinjayen Imani Da Hadin Kan Al'umma A Kan Duk Wani Karfi Na Duniya:

Mallakan makamai na daga cikin abubuwa masu muhimmancin gaske wajen samar da nasara ga kowani irin juyi da yunkuri, wato a takaice wannan makami idan har bai fi na daya bangaren da ake fuskanta ba to kuwa lalle ne kada ya gaza. Don haka ne za mu ga cewa shuwagabanni da jagororin wadannan juyi da yunkure-yunkure suna kokari wajen mallaka mafi karfi da daukakan makamai na zamani don fuskantar makiyansu. Wannan tunani kuwa ya samo asali ne sakamakon irin nisan da aka yi daga abubuwan da suka shafi imani da ruhi da al'umma ta yi, ba abin da take gani in ba karfi na zahiri ba. Wannan tunani da kuma dogaro da karfin zahiri na daga cikin dalilan da suka sanya kasashen musulmi cikin halin da suke ciki da ci gaba da shan kashi a hannun makiyansu, don kuwa su ba su da karfin kera irin wadannan makamai, a mafi yawan lokuta masu karfi kerawa makiyansu ne don haka babu yadda za su iya ba su don su yake su, idan har ma ka ga sun ba su to sun ba su ne don su kashe junansu. Wannan dai shi ne bala'in da kasashen musulmi suka shiga.

To sai dai nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran ya sanya sun farka, wato kuwa ya gabatar musu da wani sabon makami da ya fi na makiyansu, wadanda daman suna da shi amma dai sun gafala ne kawai daga amfani da shi ko kuma suna ganin ba shi da karfin da zai iya biya musu bukatunsu. To amma a halin yanzu sun fahimci cewar lalle yana iya biyan bukata. Wannan sabon makami kuwa da ya nuna kansa a juyin juya halin Musulunci na Iran shi ne 'imani da hadin kan al'umma'.

Watakila kafin nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran al'umma ba su fahimci karfin da wadannan makamai guda biyu suke da shi ba, kai ba mai kawai al'ummar ba hatta su kansu ma'abuta girman kan duniya ba su fahimci hakan ba, ko kuma idan ma sun fahimta ba su dauka tasirin nasu zai kai haka ba. Hakan ne ma ya sanya gwamnatin dagutu ta Shah, da sauran masu daure mata gindi, suka rudu daga irin karfin zahiri da suke da shi da kuma ganin karfin al'umma da Imam yake da shi ba a bakin komai ba, kwatsam kuwa sai dan hakin da suka rena ya tsole musu ido. Irin wannan tunani na karfin zahiri da ma'abuta girman kai suke da shi ne ya sanya da dama daga cikin kungiyoyin gwagwarmaya na duniya, na musulmi da ma wadanda ba haka ba, suka yanke kauna da kuma jin da wuya su iya yin nasara. To sai dai nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran ya sanya musu sabon jini da tabbatar musu da cewa lalle suna iyawa matukar dai suka dogara da karfin imanin da suke da shi da kuma hadin kansu.

Karfi irin na imani wanda ya ginu a kan wata akida ta musamman shi ne yake sanya mutum sadaukar da kansa da dukkan abin da ya mallaka don cimma manufarsa wacce ta ginu a kan wata akida da yake da ita musamman idan wannan akida ta ginu ne akan Musulunci wanda daman yake sanar da mabiyansa cewa ba su yi hasara ba matukar suka ba da rayuwa ko kuma abin da suka mallaka wajen cimma manufa, don kuwa suna da gagarumin sakamako gobe kiyama a wajen Mahaliccin kowa da komai. Duk wani juyin da ya rasa wannan akida kuwa da wuya ya kai ma manufarsa don kuwa ma'abuta yunkurin ba su da wani abin da aka tanadar musu idan da za su rasa ransu kafin isa ga manufar da suke son cimmawa.

Shi kuma karfi na hadin kai a hakikanin gaskiya cikamaki ne na karfin imani, don kuwa ko da al'umma za su sami karfin imani amma sai suka rasa karfin hadin kai, to babu inda za su je don kuwa kowa zai dinga yin abin da ya ga dama ne, a wasu lokuta ma ya yi wani abin da zai kasance cutarwa da daya bangaren. Don haka ne ma a lokuta da dama marigayi Imam yayin da yake magana kan tasirin wadannan abubuwa biyu ya kasance yana cewa:

"Wannan yunkuri ya samu nasara ne akan karfin shaidan sakamakon karfafaffen imani da hadin kanku, wannan kuwa wani taimako da shiryarwa ce ta Ubangiji Madaukakin Sarki", a wani wajen kuma yana cewa: "Wannan 'yanci da Allah Ya ba mu da kuma samun nasarar gutsure hannayen bakin haure ya samo asali ne daga imani da hadin kan da kuke da shi da kuma komawa ga Allah Madaukakin Sarki, don haka ne ni'imarSa ta rufe wannan la'umma kuma ta samu nasara", a wani wajen kuma yana cewa: "Saboda kuwarku ga Allah da kuma taken Allahu Akbar da hadin kai ya sa kuka yi galaba akan wadannan masu karfi".