Bayanai Kan Azumi
Bismillah
RAMALANA MAI ALBARKA
Hudubar Manzo Kan Azumi
Gabatarwa
Addu'ar Ganin Wata
Addu'an Suhur
Shan Ruwa
Dua al-Iftitah
Lailatul Qadri
Karamar Sallah
ADDU'OIN RANAKUN RAMALANA
Rana Ta 01-05
Rana Ta 06-10
Rana Ta 11-15
Rana Ta 16-20
Rana Ta 21-25
Rana Ta 26-30
HUKUMCE-HUKUMCEN AZUMI (Bisa Fatawan Ayatullah Khamene'i)
Ganin Wata
Sharuddan Wajibi Da Kuma Ingancin Azumi
Abubuwan Da Suke Bata Azumi
Ganganta Zama Da Janaba
Hukumce-Hukumcen Shan Ruwa
Kaffarar Azumi
Mace Mai Ciki Ko Shayarwa
Rashin Lafiya Da Kuma Hanin Likita
Mas'aloli Daban-Daban Kan Azumi
BUKUKUWAN WATAN RAMALANA
Wafatin Nana Khadijah
'Yan'uwantaka Tsakanin Musulmi
Haihuwar Imam Hasan
Yakin Badar
Daren Saran Imam Ali
Bude Garin Makka
Shahadar Imam Ali (A.S.)
Daren (Lailatul) Qadri
Ranar Qudus Ta Duniya
MAGANGANU KAN WATAN RAMALANA
Manzon Allah (s.a.w.a)
Imam Ali (a.s)
Sauran Imamai (a.s)
Imam Khumaini (r.a)
Ayatullah Khamene'i (H)

Barka da Zuwa Watan Ramalana
Bismillah

MohammedHakika watan Ramalana mai albarka yana da matukar muhimmanci a addinin Musulunci, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Shi wata ne na Allah Madaukakin Sarki". Shi ne shugaban sauran watanni na Musulunci kuma wanda yafi su daukaka. Don kuwa kamar yadda muka sani a cikinsa ne aka wajabta wa dukkan baligi namiji da baliga mace mai hankali yin azumi, wanda yana daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci. A cikin wannan wata, mai azumi baya ga sauke nauyin da ya hau kansa na yin azumin, kuma ya kan sami wani kusanci na musamman da Ubangijinsa Madaukakin Sarki da kuma samun lada mai yawa wanda zai kasance masa guzuri gobe kiyama.

Lalle yana da kyau a san cewa falalolin da suke cikin wannan wata ba wai kawai sun takaita ga yin azumi ba ne, face dai duk wani aiki na alheri da mutum ya yi a wannan wata zai kasance masa babban lada kana kuma babban guzuri da kuma daukaka. A cikin wannan wata ne aka saukar da Alkur'ani mai girma, don haka ne yake da kyau a kan dukkan musulmi da ya karanta Alkur'ani da kuma fahimtar ma'anoninsa don fahimtar dimbin ilmi da hikiman da ke cikinsa. Don ta hakan ne mutum zai sami haske da kuma tsarkaka.

Watan Ramalana wata ne na azumi, yawaita salla, kyauta da dai dukkan sauran ayyuka na ibada. Musulmi ya kan azumci dukkannin wannan wata, sai dai kuma azumi na hakika, wato ya kiyaye cinsa da shansa, bugu da kari kuma kan harshensa idanuwa, kunne, tunani da dai dukkan wasu abubuwan da aikata su zai kai shi ga samun fushin Allah Ta'ala.

Wani abin kuma da yake da kyau musulmi ya kula da shi a cikin wannan wata shi ne yawan yin du'a'i, mika wuya ga Allah, neman gafara daga zunubbai da dai sauransu, don samun daukaka da kuma kulawa ta Ubangiji.

Baya ga haka kuma a cikin wannan wata akwai wani dare mai tarin albarka da alfarma wanda duk wanda ya riski wannan dare, to ya rabauta. Wannan dare kuwa shi ne Daren (Lailatul) Qadr, wanda yafi darare dubu (kamar yadda Allah Ya ce). Wannan dare kuwa ana samunsa ne a kwanaki goma na karshe. Wasu ruwayoyi sun ce ana samunsa ne a daya daga cikin wadannan darare, wato: daren 19 ko 21 ko kuma 23, duk da cewa wasu hadisan sun fi fifita daren 23 a kan sauran dararen.. A wannan dare, ana son mutum ya shagaltu da ibada da kuma neman gafara a wajen Allah Madaukakin Sarki.

Don haka muna fatan Allah Madaukakin Sarki ya sanyamu daga cikin wadanda za su rabauta cikin wannan wata mai alfarma kuma wadanda Zai 'yantar da su a cikin watan, amin.

AYOYIN ALKUR'ANI MAI GIRMA KAN AZUMI
Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke daga gabanninku, tsammaninku, za ku yi takawa. Kwanuka kidayayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana akan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na daban. Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci sai dai wanda ya kara alheri, to, shi ne mafi alheri a gare shi. Kuma ku yi azumi ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani. (2:183-184)
Watan Ramalana ne wanda aka saukar da Alkur'ani a cikinsa yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na daban. Allah Yana nufin sauki gare ku, kuma ba ya nufin tsanani gare ku, kuma domin ku cika adadin, kuma domin ku girmama Allah a kan Ya shiryar da ku,kuma tsammaninku, za ku gode. (2:185)