Fatima bint Hazam - Ummul Banin - Uwar Abul Fadhl al-Abbas (a.s):
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ita Fatima bint Hazam bn Khalid bn Rabi' ibn Amir al-Kalbi, ta fito daga cikin gidan ma'abuta daukaka da kyawawan dabi'u, don kuwa iyayenta suna daga cikin shugabannin larabawa madaukaka. Mahaifinta shi ne Hazam bn Khalid bn Rubai'. Ana mata lakabi da Ummul Banin (Uwar 'ya'ya), wanda shi ne ma aka fi kiranta da shi. Akwai maganganu biyu kan dalilin da ya sa ake kiranta da wannan suna. Na farko dai an ce ana kiranta da wannan suna ne don kwatanta ta da kakarta Laili bint Amr wacce take da 'ya'yaye biyar maza don haka ake kiranta da uwar 'ya'yaye. Na biyu kuma cewa aka yi ita ce ta bukaci Amirul Muminina Ali (wato mijinta kenan) da ya dinga kiranta da wannan suna saboda ba ta so ya kira ta da asalin sunanta wato Fatima, don kada hakan ya tayar wa su Hasan da Husain (a.s) hankali da kuma tunatar da su mahaifiyarsu Fatima al-Zahra 'yar Manzon Allah (a.s), don haka yake kiranta da wannan suna (Ummul Banin).

Fatima Ummul Banin ta tashi ne karkashin kulawar madaukakan mahaifanta da aka sansu da kyawawan dabi'u, don haka Allah Ya arzurta ta da kyawawan dabi'u, hangen nesa da sauran siffofi kyawawa.

Haka nan lokacin da ta girma ta kasance abin misali tsakanin mata a bangaren dabi'u na kwarai da ya sa ta kasance abin yabo da son barkan kowa.

Bayan rasuwar Fatima al-Zahra (a.s) da wasu shekaru, Amirul Muminin Ali (a.s) ya bukaci ya sake yin aure don ci gaba da rayuwa. To sai dai a lokacin ya so yin auren ya so ya samu macen da ta fito daga gidan ma'abuta jaruntaka da kyawawan dabi'u, don ya samu 'ya'ya ma'abuta jaruntaka da sadaukarwa saboda aikin da ya so za su aikata nan gaba a madadinsa, don haka sai ya bukaci dan'uwansa Akil - wanda yake masani ne kan hali da yanayin larabawa - da ya zaba masa mace, ma'abuciya jarunta da dai wadannan siffofi da muka ambata a baya. Sai Akil ya ce masa:

"Ya dan'uwana! Me ya sa ba za ka nemi hannun auren Fatima bint Hazm ba, babu wadanda suka fi iyayenta jaruntaka cikin larabawa".

Don haka sai Akil, ya tafi gidansu Fatima (Ummul Banin) don shaida musu ya zo neman auren Fatima ne ga dan'uwansa Ali.

Wannan labari dai ya faranta ran iyayen Ummul Banin, saboda sun san irin matsayin Ali (a.s) da irin falalar da ya ke da ita, kuma za su sami falalar zama surukan dan'uwan Manzon Allah (s) don haka suka amince da wannan bukata ita ma kanta Fatima ta yi na'am da wannan bukata.

Bayan gudanar da dukkan abubuwan da ake bukata na aure, sai aka daura auren, amarya kuma ta tare a gidan mijinta (a.s)

Ummul Banin dai ta kasance mai nuna tsananin kauna ga 'ya'yan Fatima Hasan da Husain (a.s) ta yadda tun farko-farkon shigowarta gidan Ali (a.s) ta bayyana musu cewar ita baiwarsu ce don haka tana fatan za su karbi wannan bukata tata, hakan kuwa ta ci gaba hatta bayan haihuwar 'ya'yanta. Har ila yau ta kasance mai mika wuya da bin Iyalan Gidan Manzon Allah (s) sau da kafa, musamman Imam Husain (a.s) wanda ta kasance tana sonsa fiye da 'ya'yanta, ta yadda hatta lokacin da labarin shahadar 'ya'yanta a Karbala ya isa gare ta, ba ta damu ba, abin da ke fita a bakinta kawai shi ne 'ina dana Husain ya ke'.

Dabi'unta:

Ummul Banin (a.s) ta kasance mace ma'abuciya falala da kyawawan halaye, ta kasance masaniyar hakkokin Ahlulbaiti (a.s), ta kasance ma'abuciya fasaha, tsantsaini, zuhudu, tsoron Allah da ibada.

Baya ga wadannan halaye, Fatima Ummul Banin ta kebantu da wasu siffofi masu kyau abin yabo, da suka hada da: sadaukarwa, ta rayu da Amirul Muminina (a.s) cikin mika wuya da ikhlasi, kamar yadda ta rayu bayan shahadarsa cikin irin wannan ikhlasi gare shi da 'ya'yansa. Kamar yadda muka gani a sama, Ummul Banin ta kasance tana kauna da kare 'ya'yan Fatima al-Zahra (a.s) sama da yadda take yi wa 'ya'yanta hudu, wato Abbas da 'yan'uwansa (Abdullah, Ja'afar da Usman, kai ita ce ma ta tura su Karbala don kare dan'uwansu Imam Husain (a.s) tana mai nuna musu cewa ba za ta taba yafe musu ba matukar suka bari wani abu ya samu Husain alhali suna raye.

Bayan shekaru cikin tsarkakakkiyar rayuwa da suka hada da ibada ga Allah Madaukakin Sarki, bakin ciki mai tsawon gaske na rashi da rabuwa da bayin Allah da suka hada da mijinta mai albarka, ga kuma faji'ar rasa 'ya'yanta hudu a rana guda wajen kare Musulunci a Karbala, sannan kuma ga hidima ga bayin Allah da suka hada da mijinta Amirul Muminin (a.s) da 'ya'yansa biyu, jikokin Manzon Allah (s) kuma shugabannin matasa Aljanna, Hasan da Husain (a.s) da kuma 'yar'uwarsu Zainab al-Kubra (s), Ummul Banin ta bar duniya ne a ranar 13 ga watan Jimada Sani shekara ta 64 bayan hijirar Ma'aiki (s)

Amincin Allah Ya tabbata ga wannan baiwar Allah da ta ba da dukkan rayuwarta wajen hidima ga Musulunci, Manzon Allah (s) da Zuriyarsa, Allah Ya sanya mu karkashin inuwarsu.