ZABEN IRAN: SAKON IRANIYAWA GA BUSH
Daga
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB Tehran - Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Kada Kuri'a A Iran

Masu iya magana sukan ce wai rana ba ta karya sai dai uwar 'ya ta ji kunya, ko ba a fadi ba fitowar da al'ummar Iran, kwansu da kwarkwatarsu, suka yi a ranar Juma'ar da ta wuce (17 Yuni 2005) don kada kuri'arsu a zaben shugaban kasa karo na tara ya kasance babban bugu ga makiya Juyin Juya Halin Musulunci na kasar da kuma gwamnatin Musuluncin da ke mulki a kasar. A wannan karon ma karfin al'umma ya sake nuna kansa a fili duk kuwa da kiraye-kirayen da masu karyar kare demokradiyya da hakkokin bil'Adama suka yi wa al'ummar na kada su fito wajen kada kuri'an, to amma sai ga shi ba wai kawai ma sun yi kunnen uwar shegu ga wadannan kiraye-kiraye ba ne face ma hakan ya kara musu karfin gwuiwan fitowa da nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci da suka kafa musamman bayan kiran da (juyin) ya yi musu, sakamakon kewaye shi da makiya suka yi, da cewa: Hal min nasirin yansuruni (Shin akwai wani da zai kawo min dauki).

Idan za a iya tunawa kwana guda kafin zaben, shugaban Amurka Bush ya bayyana cewa wasu 'yan tsirarru da ba a zabe su ba ne ke mulkin Iran da toshe hanyar 'yanci da demokradiyya don haka al'ummar Iran ba za su fito zabe ba. A wautansa, wannan kalami na rashin mafadi nasa zai sanya Iraniyawa shantakewa cikin gidajensu da kin fitowa kada kuri'a, to sai dai ina, karfe tara na safe (lokacin Iran - wato lokacin fara zabe) na yi sai jama'a suka fara tuttudowa dakunan zabe don kada kuri'a da sanar da Bush da mukarrabansa cewa: ba' a shirye suke su saurare su ba, musamman ma bayan da suka ga Jagoransu - Imam Khamene'i - ya fito ya kada tasa kuri'ar, wannan dai ya tuna min da jan kunne da gargadin da kakakin Ma'aikatar harkokin wajen Iran din Hamid Ridha Asefi ya yi wa jami'an Amurka (bayan jawabin Bush da sakatariyar wajensa - Rice -) cewa: Su kula da kalaman da suke fadi don kada ranar Asabar (ranar da za a fadi sakamakon zaben) su ji kunya, hakan kuwa ya faru, kai tun ma ba a kai asabar din ba, duniya suka fara musu ihu da tula musu kasa sakamakon fitowar da al'ummar suka yi.

A hakikanin gaskiya, da za a tambaye ni ra'ayina kan wannan zabe, to da abin da zan fara cewa shi ne wannan zabe dai ya kasance babbar nasara ga al'ummar Iran, sannan hasara da kunya ga wasu jama'a guda uku:

Nasara ce ga al'ummar Iran saboda sun sami nasarar watsa kasa a idanuwan makiyansu da kuma sanar wa al'ummar duniya cewa babu wanda ya isa ya tsara musu tafarkin da za su bi, su da kansu za su zaba wa kansu yadda suke son rayuwa. Hakan kuwa shi ne abin da daman ake zaton gani daga wajen al'ummar da suka jagoranci Juyin Juya Halin da ya yi waje-rod da 'yan mulkin mallaka daga kasarsu da kuma kafa tsarin Musulunci, da kuma ci gaba da kare tsarin tsawon shekaru 26. Wani ma da muke magana da shi kan wannan batu sai ya ce min, a'a da man wannan shi ne mafi karancin abin da ake zaton gani daga al'ummar da suka yi shekaru takwas suna kare kasarsu da fatattakan 'yan wuce gona da iri a lokacin kallafaffen yaki, al'ummar da suka nade hannayen rigunarsu ba dare ba rana wajen sake gina kasarsu bayan da Saddam da iyayengijinsa suka ruguza musu ita, al'ummar da suka tsaya tsayin daka wajen….., al'ummar da suka yi tsayin daka wajen….., ni dai sai na tsaya kawai ina kallonsa yana ta lissafo abubuwan da suka yi, daga karshe dai na ce masa: "Lalle ka fadi gaskiya".

Su kuwa wadannan jama'a uku da suka yi hasara su ne:

Na farko: Makiya Juyin Juya Halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci wadanda suka yi iyakacin iyawansu wajen gani sun hana al'umma fitowa kada kuri'a, sannan kuma suka shiga bayyana cewa zaben ma ya saba wa demokradiyya, lokacin da suka fahimci gazawa da rashin nasararsu kan al'umma. Ko ba a fadi ba wadannan jama'a karkashin jagoranci Amurka sun fuskanci kakkausar mai da martani daga al'ummar Iran ranar juma'a da ta wuce, duk kuwa da cewa wannan ba shi ne karon farko da Iraniyawan suka ce wa Amurka da shuwagabanninta 'mun ki' ba kuma ba na jin zai kasance na karshe.

Na biyu: Su ne wadanda suka amince da shiftar Amurka, - shin a cikin gida suke ko a waje -, wato wadanda maimakon su karfafa gwuiwar al'umma fitowa zabe sai suka koma suna sare musu kafa da kokarin hana su fitowa. Ko shakka babu, ba su da bambanci da jama'a ta farko saboda burinsu guda ne, shi ne hana mutane fitowa zabe.

Na uku: Su ne wadanda suka yi gum da bakinsu ba su ce komai ba kan kokarin da makiyan suke yi wajen hana al'umma fitowa duk kuwa da cewa suna da ikon hakan kuma maganarsu tana da tasiri.

Ko shakka babu, irin fitowar da al'ummar Iran suka yi - mai ban mamaki - ta sake sanya Bush da sabbin 'yan mazan jiya dake tare da shi cikin halin tsaka mai wuya saboda ikirarin karya da ha'intar al'ummarsu da suke ci gaba da yi bugu da kari kan fatar da suke da ita ta cewa al'ummar Iran za su yi watsi da tafarkin Jagoransu marigayi Imam Khumaini (r.a).

Zaben ranar juma'a - wanda shi ne zabe na 26 da aka gudanar tun bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci da kuma fatattakan Amurka daga kasar - yana da tasirin gaske kan makircin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya da sauran kasashen duniya a kokarin da (Amurka) take yi na baza faratun (zaluncinta) a kan kasashen musulmi da sunan "Babban Shirin Yankin Gabas ta Tsakiya". Don kuwa babbar barazanar dake fuskantar Bush da haramtacciyar uwargijiyarsa haramtacciyar kasar Isra'ila, ita ce farkawar al'ummar da kuma riko da hakikanin koyarwa ta Musulunci. Babu wanda yake kokwanton cewa al'ummomin musulmi na duniya sun zuba idanuwa da kuma fatar alheri ga wannan zabe.

Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya jami'an fadan White House fitar da irin wadannan ikirari na su na rashin mafadi da fatan ko watakila zai yi tasiri ga al'umma don su sami cimma manufofinsu musamman bisa la'akari da matsalolin da Amurka take fuskanta a yankin, a kasar Iraki, a Afghanistan da sauransu. Sun gaza a mamaye Iraki da suka yi da sauran makirce-makircensu a kasar, bugu da kari kan take hakkokin bil'Adama da suke yi a wajajen tsare mutane na Guantanamo, Abu Ghuraib da Bagram (na Afghanistan), baya ga na cikin gida duk dai da sunan abin da suka kira fada da ta'addanci, dukkan wadannan abubuwa sun kwance wa jami'an Amurka zani a kasuwa da kuma cire musu duk wata rigar mutumcin da suke sanye da ita (idan har ma suna da itan kenan - kamar yadda wani yace). Kai madalla, inji wannan aboki nawa, da hangen nesan marigayi Imam Khumaini, Mu'assasin Juyin Juya Halin Musulunci da kuma Jagora na yanzu Imam Sayyid Ali Khamene'i da ya taimaka wajen kai Iran matsayin da ta kai.

To ko ma dai mene ne wannan fitowa da al'ummar Iran din suka yi sun tabbatar wa Bush da mukarrabansa cewa ba su fahimci al'ummar Iran ba, ko kuma sun fahimce su amma suna kokarin wofantar da hankulan al'ummar duniya ne, amma sai suka fada tarkon da suka dana. Har ila yau al'ummar sun tabbatar wa duniya cewa makomarsu ta dame su. Kamar yadda kuma suka tabbatar cewa sun yi imani da irin tsarin demokradiyyar da suka zaba wa kansu ba demokradiyyar bakin haure ba.