Imam Khumaini Da Duniyar Musulmi:
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Marigayi Imam - Dukkan Tunaninsa Shi Ne Yadda Musulunci da Musulmi Za Su Ci Gaba

Duk da cewa shekaru goma sha biyar kenan muke ciki na wafatin Marigayi Imam Khumaini, Mu'assasin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kana kuma Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci amma har ya zuwa yanzu al'ummar musulmi suna jin zafin wannan babban rashi da suka yi, to sai dai abin da ke faranta rai shi ne cewa har ya zuwa yanzu din kalamai da rubuce-rubucensa sun kasance abubuwan da suke shiryar da al'umma wajen samun nasara a wannan duniya da kuma samun kyakkyawan sakamako a rayuwarsu ta gobe. Hakan kuwa saboda Imam Khumaini mutum ne da ya kasance mai damuwa da halin da al'ummar musulmi suke ciki da kuma kokari wajen tabbatar musu da daukaka da girmansu a idon duniya.

A lokacin rayuwarsa Imam ya kasance ya kan jaddada cewa kasashen musulmi dai suna da ababe masu yawan gaske da za su iya tabbatar musu da ci gaba da daukaka ta duniya da ta lahira. Dangane da wannan batu musamman ma kan batun man fetur da Allah Ya arzurta kasashen musulmin da shi yana cewa: "…Wannan arziki mai girma na man fetur, yana hannun al'umma musulmi ne. Hakika wannan ma'adini mai muhimmancin gaske da duk wata kasar da ka ga ta ci gaba to ta samu hakan ne ta hanyarsa…..dukkan wannan abu yana hannunku ne (Ya ku musulmi)….". Bugu da kari kuma kan irin yawan mutane da fadin kasar da Allah Ya yi wa al'ummar musulmi da idan har aka yi amfani da su ta hanyar da ta dace, babu makawa da musulmi sun zamanto masu karfin da babu wani da zai iya fuskantarsu.

Abin bakin ciki, a halin da ake ciki duniyar musulmi tana fuskantar matsaloli daban-daban da suke yin kafar ungulu ga ci gaba da kuma daukakar kasashen musulmin. Yayin da yake nuna rashin jin dadi da amincewarsa da wannan yanayi, Imam (r.a) yana cewa: "Ya ku 'yan'uwana musulmi, ku san cewa kasashen yammaci ga gabashi suna kwashe mana dukkanin arzikin da Allah Ya yi mana sannan su bar mu cikin talauci da dogaro da su ta bangarorin siyasa, tattalin arziki, al'adu da ayyukan soji". A ra'ayin Imam dai tsoma baki da mulkin mallaka kasashen waje a kasashen musulmi su ne ummul aba'isin din ci bayan da kasashen musulmi suke fama da shi. Saboda fahimtar wannan lamari da Imam ya yi ne ma ya sanya a koda yaushe yake tona asirin wadannan 'yan mulkin mallaka da kokarin da suke yi na sace dukiyoyin da Allah Ya arzurta kasashen musulmi da shi.

Duk da cewa dai shekarun mulkin mallaka da sace dukiyoyin kasashen musulmi a zahiri sun kauce, to sai dai a wannan zamani da muke ciki ma manyan kasashen duniya sun fito da wasu sabbin hanyoyi na sace dukiyoyin al'umma da mallake su, a takaice dai ana iya cewa sun fito da wani sabon mulkin mallakan. A halin da ake ciki, bayan faduwar tarayyar Sobiyeti, kasar Amurka ta kasance babbar annoba ga kasashen duniya musamman ma na musulmi. Tun da jimawa dai, Imam Khumaini, saboda masaniyya ta siyasa da yake da ita, ya fahimci irin wannan hatsari da ke fuskantar al'umma, don haka ne ya sha jan kunnensu da cewa: "Mafi muhimmanci da girman hatsarin da ke fuskantar kasashen musulmi da wadanda ba na musulmi ba shi ne Amurka. Amurka a matsayinta na kasar da ta fi kowace kasa karfi a duniya ba ta yin kasa a gwuiwa wajen debe arzikin da kasashen da suke binta suka mallaka". Imam ya ci gaba inda ya yi tambaya da cewa: "Wai shin da wani hakkin ne Amurka ta ke mike hannayenta a wannan bangare na duniya, a bangare guda kuma ta tsoma baki cikin al'amurran cikin gidan kasashen musulmi da kuma son ayyana wa kasashen musulmi makomarsu? Imam Ya Koma Ga Mahaliccinsa - Sayyid Ahmad Dan Imam Yana Kuka Bayan Rasuwar Mahaifinsa (r.a)

Sanannen abu ne cewa haramtacciyar kasar Isra'ila ita ce makiya ta daban ta al'ummar musulmi. Wannan haramtacciyar kasa dai, wacce take samun goyon bayan Amurka ido rufe, sama da rabin karni kenan ta mamaye kasar musulmi ta Falastinu sannan kuma take cin gaba da kulla makirce-makirce akan sauran kasashen musulmi. Tun dai ba a je ko ina ba da fara yunkurin al'ummar Iran, marigayi Imam Khumaini ya bayyana wannan haramtacciyar kasa a matsayin 'ciwon sankara' ga kasashen musulmi, sannan kuma ya ci gaba da bayyana wa al'ummar musulmi hatsarinta da kuma irin akidarta ta wariya da mamaya. A daya daga cikin jawabansa, yayin da yake tona asirin wannan 'babbar annoba' cewa ya ke:

"Manufar wadannan mutane ita ce yada akidar sahyoniyanci da dora shi akan duniyar musulmi don mulkin mallaka da mallake arzikin kasashen musulmi, hanya guda kawai da za a bi wajen 'yantar da kai daga wannan bala'i ita ce sadaukarwa, tsayin daka da kuma hadin kan kasashen musulmi".

Yayin da kuma yake magana kan ummul aba'isin din gabar da Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila suke yi da musulmi, wanda a halin yanzu ake ganinta a fili, Imam cewa yake: Ya ku 'yan'uwana! Ya kamata ku san cewa Amurka da Isra'ila suna gaba ne da asalin tushen Musulunci, hakan kuwa saboda suna ganin Musulunci, Alkur'ani da Sunnar Ma'aikin Allah a matsayin manyan abubuwan da suke musu kafar ungulu wajen cimma burorinsu".

Imam Khumaini (r.a), a matsayinsa na uba mai rahama ga dukkan al'ummar musulmi, ya gudanar da dukkan madaukakiyar rayuwarsa ce wajen shiryar da al'ummar musulmi da 'yantar da su daga rauni da koma bayan da suke ciki. Daya daga cikin mafi muhimmancin wannan aiki nasa shi ne komar da mutane zuwa ga Musulunci da farkar da su daga barci mai nauyin da suke ciki wanda hakan ita ce asalin hadafin juyin juya halin Musuluncin da ya jagoranta. Jaddadawan da yake wajen komawa ga Musulunci yana yi ne don imanin da yake da shi cewa addinin Musulunci a matsayinsa na cikakken addini shi ne kawai hanyar da 'yan'Adam za su bi da zai magance musu matsalolin da suke fuskanta. Dangane da wannan batu an ruwaito shi yana cewa: "Dokokin Musulunci dai, shin dokoki ne na siyasa da tattalin arziki, ko kuma na zamantakewa da al'adu, dokoki ne da suke cike da kamala, wanda babu wani da zai yi mu'amala da su face sai ya so su da kuma riko da su". Daga nan sai ya ci gaba da cewa: " Matukar dai kuka yi aiki da (dokokin) Musulunci kamar yadda suke, to babu shakka daukaka tana tare da ku, don kuwa 'Daukaka ta Allah ne da ManzonSa da kuma Muminai' " .

Bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci a Iran, kasar Amurka da sauran makiya sun yi ta kokarin dukkan iyawarsu wajen ganin sun dushe hasken wannan juyi da kuma irin komawa ga Musulunci da al'umma suke yi, to sai dai kuma ina sun gagara. Duk cikin wannan lokaci, Imam ya kasance mai jan kunnen al'umma da cewa: "Dole ne ku yi kokari ku sanya idanuwa da fahimtar irin lalacewar da yammaci suka kai don sanar da sauran al'umma, sannan kuma cikin yardar Allah ku yi kokarin mayar da gurbin irin wadannan lalacewa da kyawawan dabi'u na Musulunci, don 'yan baya masu zuwa su tarbiyantu da su".

Daya daga cikin ayyukan Imam na kokarin 'yantar da al'umma daga matsalolin da suke ciki shi ne jaddada batun hadin kai tsakanin musulmi. Imam dai ya yi amanna da cewa hadin kai da aiki waje guda na daga cikin koyarwar Musulunci, inda yake cewa: "Dole ne dukkan musulmin duniya su mai da hankali kan ayoyin Alkur'ani da suka yi magana kan hadin kan al'umma. Wadannan ayoyi dai su na kiran musulmi ne da su hada kansu waje guda kana kuma su yi riko da igiyar Allah, wanda hakan shi ne Musulunci". A mahangar Imam dai hadin kai da riko da igiyar Allah shi ne hanyar kawo karshen makiya, kamar yadda yake cewa: "Ina rokon Allah da Ya sanya al'ummar musulmi su hada kansu waje guda sannan kuma gwamnatocin kasashen musulmi su farka daga barcin da suke yi don samun hadin kai tsakaninsu da kuma gutsure hannuwan kasashen duniya ma'abuta girma kai da suke son cutar da su"

Wani abin da kuma Imam ya sha kiran musulmi gare shi shi ne batun dogaro da kai da jin cewa su ma fa za su iya, don kuwa daya daga cikkin matsalolin da musulmi suke fuskanta wanda kuma ya mai she su baya shi ne batun dogaro da kayayyakin bakin haure. A ra'ayin Imam matukar dai kasashen musulmi suka yi amfani da arzikin da Allah Ya yi musu to sai dai a nema a wajensu ba wai su su nema a wajen wasu ba.

A takaice dai, duk tsawon rayuwarsa madaukakiya, ba abin da ya sa a gaba in banda kokarin ganin al'ummar musulmi sun sami daukaka, kuma haka ya yi ta yi har lokacin da Allah Ya dauke shi zuwa ga rahamarSa Madaukakin Sarki. Don haka abin da dai ya hau kan musulmin shi ne kokarin wajen ganin wannan buri na Imam ya tabbatu.

Allah dai Ya jikansa Ya kuma saka masa da alherinSa kan wannan kokari da ya yi Ya kuma tayar da shi tare da Kakanninsa (a.s), wannan dai ita ce fatarmu a wannan shekara ta 15 da wafatin (r.a)