Sulhun Imam Hasan (a.s) Da Mu'awiyya :
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Babu shakka sulhun da Imam Hasan (a.s) ya yi da Mu'awiyya bn Abi Sufyan na daga cikin bangarorin rayuwar Imam Hasan din da suka fi muhimmanci da janyo hankula da bahasi da alamomin tambaya kansa. Akwai tambayoyi da yawa da suke tasowa, irin su me ya sa Imam Hasan ya yarda ya yi wannan sulhu? Me ya sa Imam Hasan ya yarda ya yi sulhu da Mu'awiyya duk kuwa da ya riga da ya san irin yanayinsa da kuma burin da yake son cimmawa? Me ya sa bai mike tsaye kamar yadda dan'uwansa Husaini ya yi ba, ko dai ya yi nasara ko kuma ya yi shahada? Da dai sauran tambayoyi makamantan wadannan. Malamai da marubuta da dama sun yi magana kan wannan batu, kowa da irin yadda yake ganin lamarin, wasu suna kyakkyawan gani wa batu wasu kuwa akasin hakan, to sai dai abin da yake a fili cikinsa shi ne cewa Imam Hasan (a.s) ya yi wannan sulhu ne saboda maslaha ta Musulunci da suka hada da kare shi (Musulunci) da kuma musulmi fadawa cikin wani irin yanayi, fitar da hakikanin gaskiya da bayyanar da makaryaci, kare tafarkin Imamanci wanda Manzon Allah (s.a.w.a) ya gina da dai sauransu kamar yadda za mu gani a nan gaba. Don kuwa idan muka yi dubi kadan za mu ga cewa wannan rikici da ya barke tsakanin kungiyar gaskiya karkashin jagorancin Imam Hasan (a.s) da kuma ta karya karkashin jagorancin Mu'awiyya ci gaba ne na rikicin da ya barke jin kadan bayan rasuwar Ma'aiki (s.a.w.a), wato kokarin raba Ahlulbaitin Ma'aiki da jagorancin al'umma da shiryar da su. Don kuwa bayan rasuwar Ma'aiki (s.a.w.a), 'manyan mutanen' wancan lokacin sun yi amfani da wasu hujjoji marasa tushe wajen hana Imam Ali (a.s) hakkinsa na halifancin Manzo, duk kuwa da irin maganganun da Manzon din ya yi kan wannan hakki, bayan wani lokaci mai tsawo gaske da kuma yadda al'umma suka dawo wajen Imam Alin da mika masa ragamar jagorancinsu, wadannan mutane dai ba su hakura ba inda suka yi amfani da wasu hanyoyi, ciki har da fakewa da daukan fansan 'jinin halifa Usman' wanda suka ce wai an kashe shi ne 'ba tare da hakki ba', wajen sake haifar da wani sabon rikicin da kokarin kawar da Ahlulbaiti (a.s) daga wannan matsayi da Allah da ManzonSa suka tanadar musu. Har lokacin da suka samu nasarar kawar da halaltaccen halifan Ma'aiki (a.s).

To da yake dai wannan kulli na cikin zuciya, Mu'awiyya bai hakura ba, inda ya ci gaba da kulle-kulle wajen ganin ya kawar da Imam Hasan, wanda jama'a suka zaba, don ya samu damar cin karensa babu babbaka da kuma share fagen dora ashararin dansa (Yazid) a kan karagar mulki. Daga cikin irin wadannan hanyoyi da ya bi har da tara makamai, sayen manyan gari, barazana nan da can da dai sauransu. Shi kuwa a nasa bangare, Imam Hasan (a.s) wanda daman aikinsa shi ne kare wannan addini da ci gabantar da shi bugu da kari kan shiryar da jama'a, ko mulki na hannunsu ko kuma ba ya hannunsu, kamar yadda Manzo din yake cewa: "Hasan da Husaini Imamai ne sun tashi ko ba su tashi ba". To wadannan tambayoyi (da suke sama) su ne za mu yi kokarin amsawa cikin dan wannan rubutu, muna masu neman izinin yin hakan daga mahaifiyarsa Al-Zahra (a.s).

Yayin kokarin amsa wannan tambaya da bayyana dalilan yin sulhu za mu yi ishara ne da wasu abubuwa guda hudu, kamar haka:

Na Farko: Halalcin Yin Sulhu:

Dubi cikin tarihi da dokokin Musulunci zai sa mu fahimci cewa shi ba addini ne da yake kiran mabiyansa zuwa ga yaki kawai ba, a daidai lokacin da yake kiransu zuwa ga yaki da jihadi cikin yanayi na musamman, haka nan kuma ya ke kiransu zuwa ga sulhu a duk lokacin da yakin ba zai haifar da manufa da sakamako ba. Don haka sulhu abu ne da Musulunci ya yarda da shi musamman ma idan har ya yi daidai da maslahar Musulunci, kamar yadda za mug a hakan cikin rayuwar Ma'aiki (s.a.w.a) yayin day a shiga fagen fama da kafirai a Badar, Uhud, Hunain da sauransu, sannan a wani lokacin kuma ya yi sulhu da su a Hudaibiyya. A takaice muna iya cewa kamar yadda Annabi (s.a.w.a) ya yi sulhu da makiya saboda wasu dalilai, da mai yiyuwa hakan ya wuce karfin fahimtar wasu, haka nan shi ma Imam Hasan (a.s) ya yi wannan sulhu ne saboda wadansu dalilan, da mai yiyuwa ne ya wuce karfin fahimtar wasu, kamar yadda ma aka ruwaito shi yana cewa: "Abin da ya sanya Manzo Allah (s.a.w.a) ya yi sulhu da wadancan (kabilu na larabawa) shi ne abin da ya sanya ni sulhu da Mu'awiyya(1)". Don haka batun rashin ingancin ko halalcin wannan sulhu ma dai bai taso ba musamman idan muka yi la'akari da wanda ya yi sulhun shi ne Imam Hasan, wanda Imami ne Ma'asumi (a bisa akidarmu). Da farko dai idan muka duba za mu ga cewa gwamnatin Musulunci a lokacin tana da tsananin bukatuwa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali na cikin gida bayan rikice-rikicen da ta yi ta fama da su kafin sulhun, wanda rashin hakan na iya ba wa abokan gaba damar cimma manufar da suke son cimmawa. Babu shakka a fili yake cewa Imam Hasan (a.s) ya san irin wannan hali da duniyar musulmin take ciki, don haka babu abin da ya rage masa face abubuwa biyu:

  • Ko dai ya ci gaba da rikici da Mu'awiyya bala'i ya fada wa musulmi.
  • Ko kuma ya nemi hanyar sulhu don alal akalla ya kare Musulunci da fadawa cikin mummunan yanayi da yake gab da fadawa, Allah ba shi ya koma gefe ya ci gaba da shiryar da al'umma kamar yadda mahaifinsa ya yi, hakan kuwa ya yi.

A wancan lokacin Imam Hasan (a.s) ya riga da ya fahimci cewa yanayi ba zai ba shi damar ci gaba da rikici da Mu'awiyya ba, idan har ma mun dauka kenan cewa Imam din zai fuskanci Mu'awiyya, saboda irin halin yanayi da tunanin da al'ummar musulmi suke ciki. A matsayin misali a daidai wannan lokaci al'ummar musulmi, sakamakon irin abubuwan da suka ta faruwa, suna cikin yanayi na shakka da rashin fahimtar abin da ya kamata su yi. A lokacin da dama daga cikin musulmin suna ma ganin rikicin da ke gudana ba wani abu ba ne face neman mulki kawai, ba wai rikici ne tsakanin gaskiya da karya ba. Don haka babu abin da ya dace face Imam ya yi sulhu da Mu'awiyya wanda a cikin hakan ma zai iya bayyanar da gaskiya da kuma hakikanin Mu'awiyya da kuma hakikanin Imam Hasan (a.s), ta haka sai wannan cuta da take damunsu ta kawu, hakan kuwa ya faru bayan yin sulhu da kuma abubuwan da Mu'awiyya ya dinga aikatawa.

Muna iya cewa wannan sulhu da Imam Hasan (a.s) ya yi yana nuni da irin fahimtarsa da kuma daukan matsayin da ya dace a lokacin da ake cikin yanayi mai wahalar gaske. Don haka Imam Hasan (a.s) a matsayinsa na Imami Mai shiryarwa ba zai aikata wani abu da zai cutar da Musulunci da musulmi ba.

Na Biyu: Yanayi

Babu shakka yanayi na daga cikin abubuwan da suke da muhimmancin gaske wajen dauka duk wata matsaya da mutum (shugaba) zai dauka. Watakila ba mu wuce guri ba idan har muka ce kusan dukkan matsaya ta siyasa da ake dauka suna da alaka da yanayin da ake ciki ko da kuwa akwai sauran wasu batutuwa na daban. Don haka yanayi na da tasirin gaske hatta cikin matakan da Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya dauka na hana fito na fito da makiya a wasu lokuta, a wasu lokutan kuma ya ba da umarnin hakan saboda canjin yanayin da aka samu. Hakan ma Imam Ali (a.s) ya aikata bayan Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma lokacin hukumcinsa.

Don haka yanayi a wani lokaci ya kan sa a dau wata matsaya, sannan a wani lokacin kuma ya sa a janye wannan matsaya da aka dauka. A nan muna iya raba yanayi zuwa gida biyu…yanayi mai tabbatarwa da yanayi maras tabbatarwa.

     (A). Yanayi Mai Tabbatarwa: Shi ne yanayin da ake ganinsa a matsayin abin da ke taimakawa da kara wa mutum karfin gwuiwan daukan matsaya da tun farko ita ce ya kamata a dauka in da ba don wasu dalilai ba.

     (B). Yanayi Maras tabbatarwa (korau): Shi ne yanayin da zai sanya mutum daukan wata matsaya wacce ba ita ya kamata ya dauka ba amma saboda yanayi ya dauke ta don kauce wa wani yanayi mai cutarwa. Irin wadannan abubuwa su ne suka sanya Imam Hasan (a.s) daukan matsayar yin sulhu da Mu'awiyya maimaikon yakarsa, daga cikinsu kuwa akwai:

  1. Rashin tsayayyu kana muminan dakaru da za su iya fuskantar sojojin Mu'awiyya da tsayawa a gabansu, kamar yadda Imam Hasan (a.s) ya ke cewa: "Wallahi ban mika masa al'amarin ba face sai don saboda rashin mataimaka, da na samu mataimaka da na yake shi dare da rana har Allah Ya yi hukumci tsakanina da shi...(2)".

  2. Rashin hadin kai da magana guda cikin rundunar Imam Hasan (a.s). Babu shakka daya daga cikin mafi hatsarin alamar rarrabuwar kan sojoji shi ne samun sabani da banbancin ra'ayi da inda aka sa gaba. Samun wannan yanayi cikin sojojin Imam Hasan (a.s) da kuma rashin karbar umarni daga waje guda, shiga cikin yaki da irin wannan yanayi tamkar kisan kai ne, don haka ne ma Imam (a.s) yake cewa: "Hakika ina ganin mutanen Kufa a matsayin mutane ne ba abin amincewa ba, babu wanda zai dogara da su face wanda ya mika kai, babu guda daga cikinsu da ya amince da dan'uwansa(3)".

  3. Mika kai da hada baki da Mu'awiyya da da dama daga cikin sojojin Imam Hasan (a.s) suka yi musamman ma kwamandojin rundunar, a bangare guda kuma da dama daga cikin mutanen Kufa sun rubuta wa Mu'awiyya cewa: "Lalle muna tare da kai, idan ma ka so muna iya kama Hasan mu aiko maka da shi".

  4. Yaduwar fitina da jita-jita cikin rundunar Imam Hasan (a.s) sakamakon kutsawan da 'yan leken asirin Mu'awiyya suka yi cikin rundunar don rarrabata. Daga cikin irin wadannan farfaganda har da kokarin nuna cewa: Hasan yana nan yana ta shirin sulhu da Mu'awiyya a boye, don haka kada ma ku sanya kanku cikin halaka, da dai sauransu.

  5. Komawar zukatan sojojin zuwa ga batun sulhu sakamakon farfaganda da kuma sayen kwamandojin rundunar da Mu'awiyya ya yi da kudade masu yawan gaske, da ya sanya wasu daga cikin rundunar Imam Hasan (a.s) ko dai sun gudu sun bar fagen daga ko kuma sun koma cikin sojojin makiya.

Shin ya ya za a yi Imam Hasan (a.s) ya fuskanci abokin gaba mai karfi kamar Mu'awiyya da irin wadannan sojoji da mutane da suka rasa ruhin jihadi. A takaice dai ana iya cewa al'ummar Iraki a lokacin ba al'umma ce da take da kalma guda ba, al'umma ce da ta rarrabu da kuma akidu daban-daban masu karo da juna. Misali akwai mabiya Ahlulbaiti (a.s) na hakika, akwai kuma mabiya Mu'awiyya, ga kuma Khawarijawa da suke kokarin ganin bayan bangarorin biyu ga kuma mutanen da ake kira shakkakun (ma'abuta shakka) wadanda ba su da tsayayyiyar akida, a buga su nan a buga su can, sannan kuma ga ma'abuta son fitina don samun ganima da dai sauransu.

To yadda yanayi kenan ya kasance a lokacin, da suka sanya Imam Hasan (a.s) tunanin mafita daga cikin halin da ake ciki da kuma dage hannaye daga zubar da jinin musulmi. Shi ne mutum na hudu daga cikin mutanen da suka fara karban sakon Musulunci. A da dai ya kasance daga cikin masu bauta wa gumaka, amma lokacin da ya musulunta sai ya zo dakin Ka'aba ya bayyanar da Musuluncinsa, inda Kuraishawa suka ta dukkansa har sai da suka sumar da shi, bayan da ya farfado sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya umarce shi da ya koma garinsu, bayan yakin Badar da Uhud, ya dawo Madina inda ya ci gaba da zama tare da Manzo har lokacin da ya rasu, sai ya koma Sham ya ci gaba da zama, to sai dai daga baya halifa Usman ya dawo da shi ya kuma tura shi gudun hijira zuwa wani kauye da ake kira Rabaza, inda ya rasu a can shekara ta 32 bayan hijira.

Don haka Imam Hasan (a.s) ya amince da yin sulhu da Mu'awiyya bisa wasu sharudda don kare daular Musulunci da kuma rarrabuwan kai tsakanin musulmi. Wannan wata matsaya ce ta siyasa da take tabbatar da irin matsayin Imam Hasan da kuma hangen nesan da ya gada daga mahaifansa, don ko ba komai hakan zai ba shi damar bayyanar da gaskiya da kuma irin yanayin Mu'awiyya, saboda a duk lokacin da ya keta wannan yarjejeniya da aka kulla al'umma za su fahimci asalinsa, da hakan zai taimaka wa Imam (a.s) ko da kuwa a siyasance ne.

Lokacin da Imam ya ga cewa yaki ya saba wa babbar manufar duniyar musulmi, sannan kuma don kiyaye gwamnatin musulmi, hakan ya tilasta masa yin sulhu don cimma manufofin da muka yi bayaninsu a baya. A bangare guda kuma shi kansa Mu'awiyya ya fi fifita samun damar darewa karagar mulki cikin ruwan sanyi, don haka a shirye yake ya sadaukar da komai don cimma wannan manufa tasa, ta yadda hatta wasu bayanai sun nuna cewa ya aike da farar takarda ga Imam Hasan (a.s) yana bukatarsa da ya rubuta duk sharadin da yake son rubutawa don haifar da sulhu tsakaninsu(4). Don haka Imam Hasan (a.s) ya rubuta sharuddansa, duk da cewa litattafan tarihi son bambanta kan sharuddan amma dai abin da aka fi tafiya a kansu su ne:

  1. Mika halifanci ga Mu'awiyya kan zai yi aiki da littafin Allah da ManzonSa.

  2. Bayan mutuwar Mu'awiyya, Imam Hasan ne zai zama halifa, idan kuwa wani abu ya same shi to dan'uwansa Husaini ne zai zama halifa, Mu'awiyya ba shi da hakkin zaban wani.

  3. Za a daina la'antar Amirul Muminina Ali (a.s) a kan mimbari da cikin kunuti.

  4. Ware abin da ke cikin Baitul Malin Iraki ga Imam Hasan don gudanar da ayyukansa.

  5. Za a lamunce wa mutane lafiyarsu a duk inda suke, ba za a hukumta mutane da abubuwan da suka aikata a baya ba, ba za a cutar da mabiya Amirul Muminina (a.s) ba.

Wadannan dai kadan kenan daga cikin sharuddan da Imam Hasan (a.s) ya kafa wa Mu'awiyya, kuma haka ya yarda da su.

Na Uku: Maslahar Musulmi Ta Gaba Daya:

Wannan sulhu ya dogara ne akan maslahar musulmi ta gaba daya wanda a fili yake cewa a duk lokacin da wasu maslahohi na Musulunci ke cikin hatsari sannan kuma yin sulhu zai iya magance matsalar da za a iya fadawa cikinta, shari'ar Musulunci ta ba da dama a koma ga yin sulhu don cimma wannan buri da ake son cimmawa nan kusa ko kuma nan gaba. Daga cikin irin wadannan maslahohi na gaba daya na Musulunci kuwa sun hada har da:

  1. Hadin Kan Hukuma da Al'umma: Imam Ali (a.s) yana cewa: "Ku sani! Abin da kuke ki a jama'ance shi ya fi alheri a gare ku kan abin da kuke so a rarrabe". A fili yake cewa faruwar yaki a wannan lokacin, babu makawa, zai haifar da daya daga cikin wadannan sakamako guda biyu ne in ma dai a samu kafuwar gwamnatoci biyu ko kuma daya bangare ya yi nasara a kan dayan wanda hakan zai haifar da rauni da kuma rarrabuwan kan gwamnati da kuma al'umma. Dukkan wadannan abubuwa biyu dai hasara ce babba.

  2. Hana Zubar Da Jini da Kuma Kashe Wutar Fitina: A lokacin da daular Musulunci take fuskantar barazana daga waje, babu kokwanto rikicin cikin gida zai kasance babbar matsalar da za ta sanya gwamnati cikin yanayin faduwa kasa warwas. Don haka kare zubar da jinin musulmi da raunana karfinsu lamari ne mai tsananin muhimmancin gaske da ke cikin da'irar nauyin da ya hau kan al'umma musamman ma dai shugaba. Imam Hasan (a.s) a matsayin na shugaban musulmi ya san irin abin da zai iya fada wa al'umma sakamakon ayyukan Mu'awiyya da kuma irin rikice-rikicen da suka faru a baya, kamar yadda kuma ya san yanayin da daular Musuluncin take ciki ba zai iya daukan wani sabon rikici irin wannan ba, don haka yake son hana zubar da jini a kokarin da yake yi na kyautata tafarkin da ake kai. Babu shakka wannan lamari na daga cikin manyan lamurran da suka sanya Imam yarda da wannan sulhu. Imam yana cewa: "Hakika na ga cewa kare zubar da jini shi ya fi alheri daga zubar da shi, ba abin da nake nufi cikin hakan (sulhu) face maslaha da kuma tabbatuwarku(5)".

  3. Kare Wanzuwar Musulunci: Idan har kowani yaki na da wasu abubuwa na musamman da ya kan cimma, to kuwa yaki tsakanin Imam Hasan (a.s) da Mu'awiyya na nufin sanya dukkanin karfin da gwamnati take da shi cikin wani rikicin da zai kawar da samuwa irinta Musulunci a cikin gida, wanda hakan zai sanya ba za a iya fuskantar duk wata barazana daga waje ba. Don haka yin sulhu ya zama wajibi sakamakon irin hatsarin da Musulunci zai iya fuskanta daga waje sannan kuma ga hatsarin cikin gida da aka haifar da shi da sunan Musuluncin.

  4. Kokarin Gyara Tafarki: A hakikani gaskiya wannan sulhu yana nufin wanzuwar alheri tsakanin al'ummar musulmi don su sami damar dinke barakar da ta kunno kai da kuma samun dama wajen gudanar da gyare-gyare da tabbatar da koyarwa ta Musulunci da kuma wayar da kan al'umma don nesantar camfe-camfe da sabbin abubuwan da aka shigo da su Musulunci don biyan wasu haramtattun manufofi. Don haka ne za mu ga cewa bayan wannan sulhu, Imam Hasan (a.s) ya ba da himma wajen gyaran al'umma da kare su daga barazanar da take fuskantarsu da sake farkar da su daga gagarumin barcin da suke ciki.

  5. Za a lamunce wa mutane lafiyarsu a duk inda suke, ba za a hukumta mutane da abubuwan da suka aikata a baya ba, ba za a cutar da mabiya Amirul Muminina (a.s) ba.

Na Hudu: Maslahar Tafarkin Imamanci:

Tun bayan rasuwar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) wasu mutane sun yi kokari ba dare ba rana wajen ganin sun kange Ahlulbaiti (a.s) daga ba da gudummawarsu a bangaren siyasa da jagorantar al'umma duk kuwa da cewa wasiyyar Ma'aikin (s.a.w.a) da sauran nassosi na addini sun tabbatar da wajibcin matsayinsu a bangaren gudanarwar rayuwar al'umma ta yau da kullum wanda hakan ne kawai hanya guda ta kare al'umma da kuma Musulunci daga kowace irin barazana. Baya ga haka, bisa la'akari da matsayin da Ahlulbaitin suke da shi da wajibcin kare tafarkinsu, don haka ya zama wajibi ga Imam Hasan (a.s) ya yi dukkan abin da zai iya wajen kare wannan tafarki na Imamanci da tun da jimawa 'makiya' suke hankoransa.

Har ila yau bisa la'akari da cewa al'ummar musulmi suna bukatuwa da wani shugaba wanda zai dinga kula da dabi'u da al'amurransu zuwa ga madaidaicin tafarki da manufofin Musulunci madaukaka, don haka samuwar wani shugaba (imami) ma'asumi na daga cikin tafarkin kare wannan koyarwa ta Musulunci. Saboda haka idan dai har yin sulhu zai kare wannan tafarki na imamanci, to babu abin da zai hana shugaba ma'asumi daukan wannan matsaya, wanda hakan na a matsayin kare al'umma ce gaba daya daga fadawa tarkon ma'abuta son zuciya.

Dukkan wadannan dalilai da muka kawo a baya da suka hada da halalcin yin sulhu a shar'ance, yanayin da ake ciki, kare maslahar Musulunci da dai sauransu, suna daga cikin abubuwa da suka sanya Imam (a.s) ya zabi tafarkin yin sulhu, wanda ko ba a fadi ba an ga irin alherin da hakan ya haifar wa al'umma da kuma shi kansa Musulunci a yanayi na gaba daya. A gefe guda kuma Imam Hasan ya samu nasarar cimma manufofin da suka hada da hana zubar da jinin musulmi da rarraba kansu, bayyanar da matsayarsa a fili kan Mu'awiyya da rashin yarda da halalcin hukumarsa (kamar yadda sharuddan da ya kafa masa suka tabbatar), sannan kuma da fitar da hakikanin fuskar Mu'awiyya ga al'umma a fili don su fahimci shi wani irin mutum ne, musamman bayan da ya sa kafa ya take dukkan sharuddan da ya sanya hannu kansu don tabbatar da sulhun.

Allah Ya sa mu dace.





____________

(1)- Dubi Littafin Bihar al-Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 44 shafi na biyu Babin da ke magana kan dalilan sulhun Imam Hasan (a.s) da Mu'awiyya.

(2)- Bihar al-Anwar, juzu'i na 44 shafi na 147, Al-Ihtijaj na Shaikh al-Tabrisi.

(3)- Bihar al-Anwar juzu'i na 44 shafi na 24.

(4)- Tarikh al-Tabari, juzu'i na 4 shafi na 124.

(5)- Hayatul Imam al-Hasan na Bakir Sharif al-Karashi.