Haihuwar Imam Hasan Mujtaba (a.s)

An haifi Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) ne ranar sha biyar ga watan Ramalana mai albarka shekara ta uku bayan hijira. Mahaifansa kuwa su ne tsarkakan halittun nan guda biyu wato: Imam Ali da Kuma Fatima al-Zahra (a.s). Haihuwarsa ke dawuya sai aka sanar da Manzon Allah al-Mustafa (SAWA) da kuma albishir saboda wannan karuwa da aka yi, shi kuma sai ya garzaya gidan Fatima (AS) don taya murna da farin nuna farin cikinsa.

Koda isowarsa sai aka gabatar masa da wannan jariri mai albarka, Manzo ya karbe shi da hannayensa mai daraja, ya sumbace shi, ya rungume shi a kirjin sa; sai ya kira sallah a kunnensa na dama, ya yi ikama a na hagu, don sautin gaskiya ya zama farkon sautin da ya fara ratsa samuwarsa da jinsa. Sai Manzo (SAWA) ya waiwayi Ali (AS) ya ce: "Wane suna ka sa ma dana?" sai Imam Ali (AS) ya ce: "Ban kasance mai shiga gabanka ba ." sai Manzo ya ce: "Kamar yadda nima ban kasance mai shiga gaban Ubangijina ba." (Wato ma'ana ni ma ba zan gabaci Ubangiji wajen sa masa suna ba. Wannan tataunawa ba ta kai gacinta ba sai ga Wahayin Allah na saukowa ga Manzon Allah (SAWA) , wanda ke sanar da shi cewa Allah Madaukaki Ya sanyawa abin haihuwa suna Hassan.

Lokacin da kwanaki bakwai da haihuwa suka kewayo, sai Manzo (SAWA) ya yanka masa rago na radin suna, daga ciki ya ba unguwar -zoman da ta karvi haihuwarsa cinya tare da dinari daya, wannan a matsayin godiya bisa kokarinta a madadin abin haihuwa da mahaifiyarsa mai tsarki. Sannan ya kama kan abin haihuwa ya aske, ya yi sadaka da nauyin gashin shi da azurfa wanda ya yayyafe shi da wani nau'in turare da ake kira da Khaluq; sannan ya sa aka yi masa kaciya.

To wannan dai magana ke nan kan haihuwar Imam Hasan al-Mujtaba

To bayan nan kuma Imam Hasan (a.s) ya ci gaba da rayuwa karkashin kulawan kakansa Manzon Allah (s) cikin kauna da kuma girmamawa har lokacin da Manzo din ya koma ga Ubangijinsa. Hakika Manzon Allah ya kasance yana kaunar Imam Hasan nesa ba kusa, bari mu kawo kadan daga cikin hadisai da kuma maganganunsa akan Imam Hasan din (a.s):

  1. Bukhari da Muslim sun riwaito daga Barra'u ya ce: Na ga Manzon Allah (SAWA) a lokacin yana dauke da Hassan dan Ali a kafadarsa, sai na ji yana cewa: "Ya Allah, lallai ni ina son mai sonsa."
  2. Tirmizi ya riwaito daga Ibn Abbas cewa: Wata rana Manzon Allah (SAWA) ya kasance yana dauke da Hassan dan Ali (AS), sai wani mutum ya ce: 'Ka hau mafi alherin abin hawa yaro.' Sai Manzo (SAWA) ya ce: "Kuma shi mafi alherin mai hawa ba."
  3. An ruwaito daga Anas bin Malik cewa: An tambayi Manzo (SAWA) cewa: 'Wa ka fi so daga mutan gidanka?' Sai ya ce: Hasan da Husaini."
  4. An ruwaito daga A'isha ta ce: Manzon Allah (SAWA) ya kasance ya kan dauki Hassan ya rungume shi yana cewa: "Ya Allah wannan dana ne kuma ina son shi haka ina son wanda ke son shi."
  5. An ruwaito daga Jabir bin Abdullahi, ya ce: Manzon Allah (SAWA) ya fadi cewa: "Duk wanda ke son ya ga shugaban samarin gidan Aljanna sai ya kalli Hassan bin Ali."
Da dai sauran hadisai masu yawan gaske da malaman hadisai da tarihi suka kawo su, mai san karin bayani sai ya koma ga wadannan littattafa.

Ayyukan Imam Hassan (AS) sun fara bayyana a duniyar Musulunci da wuri. Mai bin yadda Imam Hassan ya tafiyar da rayuwarsa zai riski cewa Imam Hasan ya bada gagarumar gudummawarsa ne a zangogi biyu cikakku na rayuwarsa kamar haka:
  • Lokacin Mahaifinsa: Aikin Imam Hasan (AS) a wannan lokacin ya misaltu da cikakken biyayya ga mahaifinsa Imam Ali (AS) a matsayin shi (Imam Ali din) na abin koyi kuma Imam. Ya kasance yana mu'amala da shi ba kawai a matsayin da mai biyayya ba, har ma a matsayin soja mai bin oda.
    Imam Hassan (AS) ya halarci dukkan yakokin da mahaifinsa Imam Ali (AS) ya yi a Basra, Naharwan da Siffin(1), ya kuma taka muhimmiyar rawa a cikin su, inda ya shiga cikin wadannan yakoki, ya kashe wannan fitina ba bisa wata manufa ba face son Musulunci da tafarkinsa.
  • Lokacin Mulkin shi: Zango na biyu na aikin Imam Hassan (AS) a duniyar Musulunci ya fara ne daga lokacin da mahaifinsa ya mika masa akalar Imamanci, yayin da Imam (AS) ya yi wasici gare shi da cewa:
    "Ya kai dana, hakika Manzon Allah (SAWA) ya hore ni da in yi wasici da kai kuma in ba ka littafaina da makamaina kamar yadda shi ya yi wasici da ni kuma ya ba ni littafansa da makamansa. Haka ya hore ni da in hore ka da cewa idan mutuwa ta zo maka ka bayar da su ga dan'uwanka Husaini.(2)"
To bayan shahadar Imam Ali (a.s), sai jama'a suka yi mubaya'a wa Imam Hasan a matsayin Imami kana halifan Manzon Allah (s), kuma wannan labari ya yadu duk duniyar musulmi, kuma suka yi na'am da shi, in banda wasu da suke bangaren Mu'awiyyah dan Abu Sufyan.

A garin Sham kuwa, da labarin wafatin Imam Ali (AS) ya isa kunen Mu'awiya sai ya cika fadarsa da bukukuwa, ya lullube helkwatarsa da farin ciki. Sai dai al'amarin bai'ar Imam Hassan (AS) ya daga hankalin Mu'awuya, don haka sai ya kira taron gaggawa da masu ba shi shawara a dakin taronsu don tattaunawa a kan sababbin sauye sauyen da suka faru da tsara wata siyasa da za a fuskanci Imam Hassan (AS) da ita. Sai taron ya kudurta watsa 'yan leken asiri a cikin al'ummar Musulmi dake karkashin ja-gorancin Imam Hasan (AS) don a jefa tsoro da yada karerayi dangane da gwamnatin Ahlulbaiti (AS); kamar yadda masu halartar taron suka kuduri cewa jam'iyyar Mu'awuya ta aiwatar da wani aiki mai fadi na jan hankulan masu fada-a-ji cikin gudunar da al'amuran Iraki, wannan kuwa ta hanyar bayar da rashawa, alkawurra masu ruda hankali, kyaututtuka, tsoratarwa, barazana da sauran irinsu.

To wannan makirci na Mu'awiyyah da mutanensa kuwa ya ci nasara, inda da dama daga cikin sojojin Imam Hasan din suka rudu, suka mika wuya wa duniya suka yi hasarar lahirarsu. Lamarin da dai ya tilasta wa Imam Hasan din yarda da yin sulhu da Mu'awiyyah.

Bayan wannan sulhu ma dai, Mu'awiyyan bai bar Imam Hasan ba, don yana ganin shi a matsayin babbar barazana ga burinsa na nada ashararen dansa Yazid (L) akan al'umman musulmi. Don haka ya kulla makirci da matar Imam Hasan din mai suna mai suna Ja'adatu bint Ash'ath ta sa masa guba a cikin abinci, inda ya yi shahada a ranar 7 ga watan Safar shekarar ta hamsin bayan hijira.

Imam Hassan (AS) ya yi wasici da a bisne shi a kusa da kakansa Manzon Allah (SAWA). Sai dai Umayyawa, karkashin Marwan bin Hakam da ma wasu na daban, sun hana aiwatar da hakan, yayin da suka dage wajen ganin sai sun raba tsakanin Manzon Allah (SAWA) da jikansa, dan gaban-goshin shi kuma masoyin shi Hasan, shugaban samarin gidan Aljanna. Wannan ya sa dole Ahlulbaiti (AS) suka tafi suka bisne shi a Makabartar Baki'a.

Amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya Abu Muhammad, wanda aka zalunta a rayuwarka da bayan shahadarka.






____________
(1)- A Basra da A'isha, Nahrawan da Khawarijawa, kana Siffin kuma da rundunar "Batattu" karkashin jagoranci Mu'awiyyah bn Abi Sufyan.
(2)- Duba Hayat Imam al-Hasan na Bakir Sharif al-karashi; da Sheikh al-Dabrisi, cikin I'ilam al-Wara, shafi na 206 a babin dake magana a kan nassosin dake tabbatar da Imamancin Hasan (AS) kamar yadda ya fitar daga Kashf al-Gummah fi Ma'arifatul-A'immah, juz'i na 2, shafi na 155.