ALWALA A TAFARKIN AHLULBAITI {A.S.}



Wajibi ne kafin mutum yayi salla ko kuma taba Alkur'ani mai girma, sunan Allah, ManzonSa, Imamai da sauran Annabawa (a bisa ihtiyati)..... yayi alwala. Don haka alwala tana da muhimmancin gaske a cikin rayuwarmu ta yau da kullum.
A sabili da haka ne muka tanadi wannan fili don nuna yadda ake alwala a tafarkin Ahlulbaiti (a.s.) wadanda sune Igiyar Shiriya wadda Allah Madaukakin Sarki Ya umurce mu da riko da ita.
Don haka yanzu sai mai karatu ya gyara zama don karanta yadda ake alwalar, a sha karatu lafiya.




  • Bayan mutum ya tanadi ruwansa mai tsarki, sai ya fara wanke tafin hannuwansa, daga nan sai ya kurkure bakinsa. To amma dai duk hakan mustahabbai ne, ma'ana ba sa cikin alwala, don haka koda mutum ya barsu babu wata matsala.
  • To amma asalin alwalar, ga yadda take:

    Mutum zai fara ne da wanke fuskansa, tun daga mafarin gashi har zuwa haba, kana kuma fadinsa shi ne fadin dake tsakanin babban yatsan hannu da manuniya (koda yake an so mutum ya wuce hakan don samun yakini). Ana yin wankin ne sau guda (da sharadin ko ina ya samu ruwa) ko kuma sau biyu. To amma alwala tana iya baci idan aka wuce hakan. Kuma yana da kyau a fahimci cewa ana yin wankin ne daga sama zuwa kasa, akasin hakan yana iya bata alwala. (Dubi wancan hoton ).


    Daga nan kuma sai a wanke hannun dama, shi ma sau guda (idan har ruwan ya gama ko ina) ko kuma sau biyu. Wankewa fiye da hakan yana iya bata alwala. Abin nufi da hannu anan shi ne tun daga gwuiwan hannu zuwa kan yatsu. Kuma yana da kyau a fahimci cewa ana yin wankin ne daga sama (wato daga gwuiwan hannun) zuwa kasa (kan yatsun hannu), kuma akasin hakan yana iya bata alwalar. (Dubi wancan hoton)


    Daga nan kuma sai ya wanke hannun hagu kamar yadda ya wanke na dama.

    Daga nan sai ya shafi kansa da sauran damshin da ya rage a hannun bayan wanke hannunsa na hagu. Yana da kyau a fahimci cewa, ba a sake diban wani ruwa ko kuma taba wani ruwa kafin a shafi kan, idan aka yi haka to alwala tana iya baci, don haka dole ne a yi shafan da sauran damshin ruwan da ya saura a hannun. Ana shafan kan ne daga tsakiyar kai har zuwa mafarin gashi, kuma da hannu daya ake yi. (Dubi wanncan hoton don karin bayani):


    Bayan haka kuma sai a shafi kafar dama da sauran damshin da ya rage daga shafan kai. Anan ma yana da kyau a fahimci cewa, ba ya inganta a sake taba wani ruwa don yin shafan kafa, don hakan yana bata alwalar. Don haka dole ne ayi shafan da sauran damshin dake hannu. Kuma ana yin shafan ne daga kan yatsun kafa har ya zuwa tudun nan dake kafan mutum. (Dubi wancan hoto, don karin bayani):


    To daga nan kuma sai ya shafi kafar hagu kamar yadda ya shafi na dama.

  • To Mai karatu alwala kenan a tafarkin Ahlulbait (a.s.)


    Matsa Wannan Alama Don Komawa Sama