SALLA A TAFARKIN AHLULBAITI {A.S.}


Kiran Salla

Ikaman Salla

Salla






KIRAN SALLA

Allahu Akbar. Allahu Akbar. Allahu Akbar. Allahu Akbar

الله اكبر الله اكبر الله اكبر الله اكبر

Ashhadu Allailaha illallah . Ashhadu Allailaha illallah.

اشهد ان لا اله الله . اشهد ان لا اله الا الله

Ashhadu Anna Muhammadar Rasulullah . Ashhadu Anna Muhammadar Rasulullah.

اشهد ان محمدا رسول لله .اشهد ان محمدا رسول لله

Ashhadu Anna Aliyan Waliyyullah . Ashhadu Anna Aliyan Waliyullah.

اشهد ان عليا ولي الله . اشهد ان عليا ولي الله

Hayya Alas Salah . Hayya Alas Salah.

حي على الصلاة . حي على الصلاة

Hayya Alal Falah . Hayya Alal Falah.

حي على الفلاح . حي على الفلاح

Hayya Ala Khairil Amal . Hayya Ala Khairil Amal.

حي على خير العمل . حي على خير العمل

Allahu Akbar. Allahu Akbar.

الله اكبر . الله اكبر

La ilaha Illallah . La Ilaha Illallah

لا اله الا الله . لا اله الا الله






IKAMAN SALLA

Allahu Akbar. Allahu Akbar.

الله اكبر . الله اكبر

Ashhadu Allailaha illallah . Ashhadu Allailaha illallah.

اشهد ان لا اله الله . اشهد ان لا اله الا الله

Ashhadu Anna Muhammadar Rasulullah . Ashhadu Anna Muhammadar Rasulullah.

اشهد ان محمدا رسول لله .اشهد ان محمدا رسول لله

Ashhadu Anna Aliyan Waliyyullah . Ashhadu Anna Aliyan Waliyullah.

اشهد ان عليا ولي الله . اشهد ان عليا ولي الله

Hayya Alas Salah . Hayya Alas Salah.

حي على الصلاة . حي على الصلاة

Hayya Alal Falah . Hayya Alal Falah.

حي على الفلاح . حي على الفلاح

Hayya Ala Khairil Amal . Hayya Ala Khairil Amal.

حي على خير العمل . حي على خير العمل

Kadkamatis Salah . Kadkamatis Salah.

قد قامت الصلاة . قد قامت الصلاة

Allahu Akbar. Allahu Akbar.

الله اكبر . الله اكبر

La ilaha Illallah . La Ilaha Illallah

لا اله الا الله . لا اله الا الله






SALLA

Bayan an gama ikaman salla, sai a kabbara salla, hakan kuwa bayan daura niyya ne (wato bayan mutum ya ayyana sallar da zai yi, asubahi ce ko kuma azahar ko kuma ......). Ma'ana sai mai salla yace Allahu Akbar. (kamar yadda wannan hoto na kasa ya nuna)



Bayan kabbara salla (fadin Allahu Akbar), sai mai salla ya karanta Fatiha da Sura, wato Suratul Fatiha da wata sura ta cikin Alkur'ani mai girma, misali Suratul Tawhid (sai dai kada a mance ita Sura dole ne a karanta ta gaba dayanta, idan aka karanta wani sashi na sura aka bar wata, to hakan baya isarwa, kuma dole ne ayi Bismillah wato: Bismillahir Rahmanir Rahim, a farkon karanta kowace sura, wato dole ne yayin da mutum zai fara karanta Fatiha yayi Bismillah, haka nan ma lokacin da zai karanta Surar da zata biyo bayan Fatihar, kuma ana yin karatun ne a tsaye kyam. Dubi hoton da ke gaba).


Bayan mai salla ya gama karantun Fatiha da Sura, sai yayi kabbara ya tafi zuwa ruku'u.

Bayan ya daidaitu cikin ruku'u, sai ya karanta wannan zikirin, sau guda, wato:Subhana Rabbiyal A'ala wa bi hamdihi . Ko kuma ya karanta wannan zikirin sau uku, wato: Subhanallah, Subhanallah, Subhanallah. Koda yake yana da kyau a fahimci cewa kowani daya daga cikin wadannan zikiri guda biyu mai salla ya karanta ya wadatar, kana kuma mai salla yana iya karanta su dukkansu biyun idan ya so. Kana kuma an so bayan karanta wadannan zikirori ko kuma daya daga cikinsu, mai salla yayi salati wa Manzon Allah da Alayensa, wato yace:Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Aali Muhammad, koda yake hakan ba wajibi ba ne.


To bayan mai salla ya gama wannan zikiri, sai ya dago daga ruku'u yana mai cewa Samiallahu Liman Hamidahu.

Kana bayan ya tsaya kyam ya daidaita sai yayi Kabbara (Allahu Akbar), daga nan sai ya tafi zuwa sujada.

Bayan ya daidaita a cikin sujada, sai ya karanta zikirin cikin sujada, wato yace: Subhana Rabbiyal A'ala wa bi Hamdihi sau guda, ko kuma yace: Subhanallahi, Subhanallahi, Subhanallahi, sau uku. Koda yake yana da kyau a fahimci cewa kowani daya daga cikin wadannan zikiri guda biyu mai salla ya karanta ya wadatar, kana kuma mai salla yana iya karanta su dukkansu biyun idan ya so. Kana kuma an so bayan karanta wadannan zikirori ko kuma daya daga cikinsu, mai salla yayi salati wa Manzon Allah da Alayensa, wato yace:Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Aali Muhammad, koda yake hakan ba wajibi ba ne, kamar yadda muka bayyana a cikin ruku'u. (Dubi wancan hoton don ganin yadda ake sujada)


To bayan mai salla ya gama hakan, sai ya dago daga sujada, ya zauna, bayan ya daidaita a zaune (kamar yadda wancan hoton ya nuna), sai yace Allahu Akbar, Astagfurullah Rabbi wa atubu ilaihi, Allahu Akbar . Daga nan sai ya tafi zuwa sujada ta biyu.


Bayan ya daidaita, sai ya sake karanta zikirin sujada kamar yadda yayi a sujada ta farko.

Bayan ya gama zikirin, sai ya dago daga sujadan ya dan zauna kadan yana mai cewa Allahu Akbar. Daga nan sai ya mike don kawo raka'a ta biyu, yana mai cewa:Bi haulillahi wa quwatihi aqumu wa aq'ud.

Bayan ya mike kana kuma ya daidadita sai ya fara karatu, wato ya karanta Fatiha da Sura, kamar yadda yayi a raka'a ta farko.

Bayan ya gama karatun, to a wannan karon kan kafin ya tafi ruku'u, an so yayi "Qunut", wato ya daga hannunsa sama yana mai yin addu'a. Yana da kyau a fahimci cewa babu wata takamammiyar addu'a da aka ce dole sai ita mai salla zai karanta a cikin Qunuti, yana iya karanta kowace addu'a ya ga dama, misali:Rabbana Atina fid Dunya hasana wa fil Akhirati hasana wa qina azaban nar. An so bayan ya gama addu'an yayi salati wa Manzon Allah da Tsarkakan Alayensa (a.s), wato yace: Allahumma Salli Ala Muhammad wa Aali Muhammad. (Dubi wancan hoton don ganin yadda ake Qunutin)


Bayan ya gama addu'an sai yace: Allahu Akbar, sai ya tafi zuwa ruku'u.

Bayan ya daidaita cikin ruku'un, sai ya aikata kamar yadda ya aikata a ruku'un farko.

Bayan ya gama sai ya dago ya aikata kamar yadda ya aikata a raka'a ta farko kana sai ya tafi zuwa sujada, kamar yadda ya aikata a raka'a ta farko.

To lokacin da ya tafi sujada, sai ya aikata kamar yadda ya aikata a sujadan raka'a ta farko.

To bayan ya gama wadannan sujada guda biyu, sai ya dago ya zauna don karanta "Tashahhud" (Tahiyya), wato yace:Ashhadu An Lailaha illallahu wahdahu la sharika lahu wa Ashhadu anna Muhammadan Abduhu wa Rasuluhu, Allahumma Salli Ala Muhammad wa Aali Muhammad.

To anan idan sallar ta Asuba (Safiya) ce, sai yayi sallama, wato ya gama salla kenan. Ita sallama tana nan kamar haka ne: Assalamu Alaika Ayyuhan Nabiyu wa Rahmatullahi wa Barakatuhu, Assalamu Alaina wa ala ibadillahis Salihin, Assalamu Alaikum wa rahmatullah wa Barakatuhu. To wannan ita ce sallama.

To idan kuwa ba ta Asuba ba ce, bayan ya gama Tahiyya, sai ya mike don kawo sauran raka'o'in da suka saura yana mai cewa: Bi haulillahi wa quwatihi aqumu wa aq'ud.

To bayan ya mike tsaye kana kuma ya daidaita, sai ya fara karatu. To amma a wannan karon Fatiha kawai zai karanta banda sura. Ko kuma in ya ga dama a maimakon karanta Fatihar, sai ya karanta wadannan zikirori sau uku. Zikirorin kuwa su ne kamar haka: Subhanallahi, Walhamdu Lillahi, wa La ilaha Illallahu Walllahu Akbar.

Bayan ya gama hakan, sai yayi kabbara ya tafi zuwa ruku'u.

Bayan daidaituwa cikin ruku'un, sai ya aikata abin da ya aikata a cikin ruku'un da ya gabata.

Daga nan sai ya dago, ya aikata kamar yadda ya aikata a raka'o'in da suka gabata.

Daga nan sai ya tafi zuwa sujada kamar yadda ya aikata a raka'o'in da suka gabata.

Bayan ya daidaitu a cikin sujada, sai ya aikata abinda ake aikatawa a cikin sujada kamar yadda ya gabata.

To bayan ya kare, idan sallar ta Magariba ce, to anan ma sai yayi sallama, kamar yadda ya gabata, idan kuwa sallar Azahar, ko La'asar ko Lisha ce, to sai ya mike don kawo raka'a ta karshe.

To idan sallar ta wadannan salloli ce, bayan ya mike, sai ya aikata kamar yadda ya aikata a raka'a ta uku, kana ya zauna don yin Tahiyya da kuma sallama, kamar yadda ya gabata.

To wannan ita ce salla kenan a takaice a bisa tafarkin Imaman Shiriya (a.s), wato Mazhabar Ja'afariyya.

Sai dai yana da kyau a fahimci cewa, an so a sujada ta karshe ta kowace salla, mai salla yayi salati wa Annabi da Alayensa (a.s.) da kuma yin addu'a, to amma hakan bayan ya gama zikirin da ake yi ne a cikin sujadan. Kuma ita ma dai wannan addu'a ba a kebance wadda za a yi ba, sai dai anso mutum ya zabi daya daga cikin addu'o'in da aka ruwaito daga wajen A'imma (a.s.).


Matsa Wannan Alama Don Komawa Sama